TARIHIN RUWAN ZAMZAM DA KUMA FA'IDAR SHAN RUWAN ZAMZAM. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

TARIHIN RUWAN ZAMZAM DA KUMA FA'IDAR SHAN RUWAN ZAMZAM

Annabi Ibrahim عليه السلام
ya zauna tare da matarsa  Saratu  عليها السلام
a Kasar Falasdinu tsawon lokaci amma ba su samu haihuwa ba.

Ita kuma tana fatan Allah Ya baiwa Annabi Ibrahim  عليه السلام wanda zai gaje shi.

Don haka sai ta ba shi Baiwarta mai suna Hajara  عليها السلام
  ya aura. 

Sai Hajara  عليها السلام
ta haifar masa da mai suna Isma'ila  عليه السلام.

Don haka Sai Annabi Ibrahim  عليه السلام 
da matarsa Saratu  عليها السلام 
sukay farin ciki sosai da samun wannan da.

Sai Allah Madaukakin Sarki Ya umarci Annabi Ibrahim
 عليه السلام
ya dauki matarsa Hajara da jaririnta Ismail ya kaisu inda garin Makka yake a yanzu.

Sai Annabi Ibrahim ya bi umarnin Allah Madaukakin Sarki ya cewa matarsa ta zo ta raka shi unguwa.

Sai ta dauko jaririn nata ta goya shi, ta bi Annabi Ibrahim  عليه السلام
suka cigaba da tafiya. Ba ta san inda za a je ba amma saboda biyayya tana biye da shi.

Har saida suka iso daidai garin Makka. A lokacin babu gini ko daya a wajen. Ba mutane, ba bishiyoyi, ba ruwa, ba abinci, ba tsuntsu, ba wata dabba, ba komai a wajen sai Sahara da duwatsu.

Sai Annabi Ibrahim  عليه السلام
yay mata umarni ta zauna a wajen.

Sai ta zauna. Shi kuma ya juya yay tafiyarsa.

Sai ta kwalla masa kira ta ce " Ya Annabin Allah!, ka kawo mu nan wajen, ba abinci ba ruwa ba kowa a wajen kuma ka juya ka tafi ka bar mu".

Sai Annabi Ibrahim   عليه السلام
ya tasaya, ba tare da ya juyo ya kalleta ba kuma bai ce mata komai ba.

Sai ta sake ce masa " Ko Allah ne Ya umarce ka ka kawo mu nan?".

Sai ya ce mata "E".

Sai ta ce masa "To je ka ba komai. Tunda Allah ne Ya sa ka kawo mu na san zai kula da mu".

Sai Annabi Ibrahim  عليه السلام
ya tafi ba tare da waiwayo ya kallesu ba, saboda kada tausayinsu ya kama shi ya kasa zartar da umarnin Allah.

Don haka yay musu addu'a ya wuce abinsa.
.
.
Bayan Annabi Ibrahim  عليه السلام ya tafi, sai Jaririn Hajara 
  عليها السلام
ya saka kuka, yana bukatar ruwa.

Sai ta tashi ta fara zagayawa cikin Sahara da cikin duwatsu ko za ta samu ruwa amma ko alamar ruwa babu.

Shi kuma jariri yana cigaba da tsalla kuka.

Sai tay ta zagaye tana dubawa.
Da akwai wasu manyan duwatsu da ake kira Safa da kuma Marwa. Sai ta hau kan dutsen Safa ta lelleka ko ina ko zata hango ruwa amma bata hango.

Sai ta sauko ta hau dutsen Marwa ta lelleka ko zata hango inda ruwa  yake amma bata hanga ba.

In ta hau ta sauko sai ta zo ta duba yaronta ta sake komawa.

Sai da tay kaikawo tsakanin Safa da Marwa sau bakwai tana hawa dutsinan tana saukowa amma ba ta hango inda ruwa yake ba.

Shi kuwa Jaririn wato Annabi Isma'il  عليه السلام
yana cigaba da kuka yana shure-shure da kafafuwansa irin yadda jarirai suke yi.

Tausayinsa ya kama ta ta zauna ta kura masa ido tana jira ta ga yadda Allah Zai yi da su.

Kawai sai ta ga ruwa yana 6ul6ulowa daga inda danta yake shusshura kafarsa.

Sai tay maza ta tashi tana tare ruwan, tana ce masa "Taru! , taru!, taru!"

Ma'ana ruwan ya taru kada ya kwaranye.

Sai ruwan yay ta taruwa yana dada yawa har sai da ya zama kogi.

Da yaren su Hajara  عليها السلام
idan za a cewa abu ya taru sai a ce 'Zam'

Don haka sai tay tacewa "Zam!, zam!, zam".

Shi kuwa ruwa yana taruwa.

Sai Hajara  عليها السلام
ta baiwa `Dan ta ruwa ya sha kuma ta samu ruwan amfani.

Sai ga tsuntsaye ma sun fara zuwa kogin suna shan ruwa.

Ana nan watarana sai wasu Larabawa da ake kira Jur'hum suka zo wucewa ta Sahara, sai suka hango tsuntsaye suna shawagi a sararin Samaniya. Sai sukay mamaki. Domin sun san ba a ganin tsuntsaye a Sahara, saidai idan akwai ruwa a wajen.

Saboda haka sai suka je suka duba. Sai kuwa suka samu wannan Baiwar Allah ita kadai da Jaririnta. Sai su ka tambaye ta labarinta  ta gaya musu.

Sai suka ce "To za mu zauna tare da ke a wannan guri amma wannan ruwan na ki ne, tunda ta dalilinki ya samu".

Don haka sai suka zauna a wannan waje. Idan suna bukatar ruwa sai su baiwa Hajara abinci ita kuma ta ba su ruwa.
.
.
FA'IDODIN RUWAN ZAMZAM GUDA 36.

1-ZAMZAM, MALAIKA JIBRILUNE YA TONA RIJIYARSA.

2 ANNABI ISMAILA NE YA FARA SHAN RUWANZAMZAM.

3 ZAMZAM SHINE ASALIN KAFUWAR BIRNIN MAKKA

4 DA ZAMZAM AKA WANKE ZUCIYAR ANNABI MUHAMMAD صلى الله علي وسلم.

5 BABU RUWAN DA YA FISHI DARAJA, A DORAN KASA. 

6 ANNABI MUHAMMAD صلى الله عليه وسلم YA SHA RUWAN ZAMZAM.

7 ANNABI MUHAMMAD صلى الله عليه وسلم YA ZUBASHI A JIKINSA.

8 ANNABI MUHAMMAD صلى الله عليه وسلمYAYI GUZIRIN SA ZUWA MADINA.

9 ANNABI MUHAMMAD صلى الله عليه وسلم 
YACE ,RUWAN ZAMZAM ZAKA SAMI
BUKATAR DA KASHA SHI, SABODA ITA.

10 NANA AISHATU رضي الله عنها
, TANA GUZIRIN ZAMZAM. 

11 SABODA DARAJAR RUWAN ZAMZAM, MALAMAI
SUKAYI SABANI GAME DA WANKA DA SHI, DA
ALWALA DA TSARKI DA WANKE NAJASA.

12 SABODA DARAJAR RUWAN ZAMZAM MALAMAI
SUKAYI SABANI DA SHI DA RUWAN KAUSAR WANNE
YAFI DARAJA?!

13 MAL IBN HABIB BAMALIKI  YACE
 "ANSO GA WANDA
YAYI HAJJI, YA YAWAITA SHAN ZAMZAM, SABODA
SAMUN ALBARKA, YAYI ALWALA YAYI WANKA.

14 SHAIK ALBANIY YACE, YA KAMATA ALHAJI, YAYI
GUZURI DA ZAMZAM, DOMIN NEMAN ALBARKA,DOMIN
ANNABI MUHAMMAD صلى الله عليه وسلم
YAYI GUZIRIN SA A CIKIN GORA DA SALKA ZUWA MADINA, YANA ZUBAWA MARASA LAFIYA YANA
SHAYAR DA SU.

15 MAL ANNAWAWIY, YACE , MAZAHABARMU KAMAR
TA JAMHURIN MALAMAI, BABU LAIFI AYI WANKA DA
ZAMZAM, KUMA AYI ALWALA.

16 MAL WAHAB IBN MUNABIH YACE: ZAMZAM ABIN SHAN MASU NAGARTA, YANA TSAYAWA A MATSAYIN
ABINCI DA ABIN SHA, KUMA WARAKA DAGA LARURA.

17 MAL KHALIL, A CIKIN MUKTASAR YACE : YANA DAGA
CIKIN ABINDA AKE SO GA ALHAJJI, YA YAWAITA SHAN
ZAMZAM.

18 ACIKIN SHARHIN AN SANHURIY YACE: YANA DAGA CIKIN ABINSO, YAWAITA SHAN ZAMZAM, DA ALWALA,
DA WANKA, DA YAWAITA ADDUA A LOKACIN SHAN
ZAMZAM GA ALHAJI.

19 AL IMAM SHAFII, YACE: MUSTAHABBI NE YAWAITA
SHAN ZAMZAM.

20 MALAMAN SHAFI'AWA SUNCE: MUSTAHABBI NE SHAN ZAMZAM, DA YAWAITA SHAN SA, KUMA ANSO MUTUM
YA SHIGA CIKIN INDA RIJIYAR ZAMZAM TAKE, YA KALLI
RUWAN, YA DEBO DA GUGA, YA SHA YA ZUBA AKANSA.
DA FUSKARSA, DA KIRJINSA, KUMA YAYI GUZURI DA
SHI.

21 MAL HASANUL BASARI YACE: IDAN AN SHA RUWAN ZAMZAM AYI ADDUA, YANA CIKIN GURARE 15 DA AKE
SA RAN KARBAR ADDUAR MASU AIKIN HAJJI, SUNE
WAJAN DAWAFI, MULTAZAM, KARKASHIN INDARARO,
CIKIN KAABA, ZAMZAM, KAN SAFA, KAN MARWA,
CIKIN SAAYI, BAYAN MAKAMU IBRAHIM, MUNA, FILIN
ARFA, MUZDALIFAH, JAMRA GUDA BIYU TA FARKO DATA BIYU ANA TSAYAWA AYI ADDUA.

22 ABDULLAH DAN ABBAS RA, IDAN YA SHA ZAMZAM
SAI YAYI ADDUA YACE: YA ALLAH KA BANI ILMI MAI
AMFANI , DA ARZIKI MAI YALWA, DA WARAKA DAGA
DUKKAN LARURA.

23 ABDULLAH DAN MUBARAK IDAN YA SHA ZAMZAM SAI YA KALLI GABAS YAYI ADDUA YACE: "YA ALLAH
MANZON ALLAH صلى الله عليه وسلم
YACE, RUWAN ZAMZAM ZAKA
SAMI BUKATAR DA KASHA SHI SABODA ITA, TO GANI
NA SHA, KA RABANI DA KASHIRWA RANAR
ALKIYAMA".

24 RUWAN ZAMZAM YANA MAGANIN ZAZZABI DA MASHASHARA.

25 RUWAN ZAMZAM YANA ZAMA DALILIN KANKARE
ZUNUBI WANDA YASHA DA NIYAR TUBA

26 RUWAN ZAMZAM YANA KARA KARFIN HADDA,
WANDA YAKE SHA DA NIYAR HAKA, KAMAR YADDA AL
IMAM SUYUDIY YAYI YA ROKI ILMIN FIQHU DA HADIS. 

27 RUWAN ZAMZAM YANA KARA KARFIN MUTUM WAJAN
MU'AMALA DA IYALI.

28 SHAN ZAMZAM ALAMACE TA IMANI.

29 RUWAN ZAMZAM YANA MAGANIN YAWAN JIRI.

30 WANKE FUSKA DA ZAMZAM YANA KARA KARFIN
IDO. 

31 SHAN ZAMZAM YANA KARA KARFIN ZUCIYA.

32 SHAN ZAMZAM YANA TAFIYAR DA YAWAN FIRGICI
DA TSORO.

33 SHAN RUWAN ZAMZAM YANA RAGE GIRMAN KAI.
YANA HORE ZUCIYA.

34 KALLON RUWAN ZAMZAM YANA DA AMFANI. 

35 MAL ALBANIY YACE: YA GAMU DA WATA LARURA
WANDA LIKITA YACE SAI ANYI MASA AIKI, AMMA
KAFIN ZUWAN RANAR AIKIN, DA YA DUMFARI SHAN
RUWAN ZAMZAM, DA LOKACIN AIKIN YAYI, SAI AKA CE
BABU CUTAR YA WARKE. 

36 MAL IBNUL QAYYIM YA KAWO A CIKIN LITTAFIN SA. ZADUL MAAD, CEWA: YA GAMU DA LARURA A MAKKA
YA RASA LIKITA, SAI YA DEBI RUWAN ZAMZAM YANA
KARANTA FATIHA YASHA, NAN TAKE YA WARKE.
.
.
Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846. 

Comments

Popular Posts