AMFANIN ƘUSƊUL HINDI. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
AMFANIN ƘUSƊUL HINDIY
★ Maganin tari.
A samu garin Qusdul Hindiy rabin cokali, a hada da Kanumfari kamar kwaya bakwai a daka a hada da Zuma. Sai a zuba a ruwan dumi a sha safe da yamma.
★ Maganin Sanyi.
Garin Qusdul Hindiy a hada da Ganyen Raidore da yayan Raidore da saiwarsa a tafasa a dinga sha kullum har kwana bakwai.
★ Maganin Ciwon kai.
A hada Qustul Hindiy da ruwan kabewa a tafasa a shafa a goshi sau biyu kullum.
★ Maganin Ciwon ciki.
A hada garin Qusdul hindiy da garin Rawaya da garin Sana Makiy dukkansu ya zama yawansu daya. Sai a dinga sha da koko ko a jika da ruwa. Babba cokali daya. Yaro rabin karamin cokali.
★ Qarfin Maza.
A hada garin Qusdul Hindiy da dakakken Muruci da garin Kashe Zaqi da Kanunfari a dinga zuba rabin cokali a shayi ba Madara.
★ Naquda.
Don Saukaka Naquda a tafasa Garin Qusdul hindiy idan ya huce sai a zuba zuma a baiwa mai naquda ta sha.
★ Maganin ciwon ga6o6i.
A tafasa Qusdul Hindiy a sha a shayi ba madara.
★ Matsalar al'ada.
A zuba Ma'ul Khal cokali daya a cikin garin Qusdul hindiy a hada da garin Hulba cokali daya. Sai a tafasa a sha.
★ Maganin Aljanu.
A hada garin Qustul Hindiy da garin Ray'han a daka su. Sai a dinga shaqawa mara lafiyar a hanci. Za a ji yana atishawa Aljanun suna guduwa.
Ko kuma a hada Qusdul Hindiy da garin Raihan da 6awon lemon Tanderu a dinga yiwa mara lafiyar hayaqi da shi sau biyu kullum.
AMMA A KULA.
Mai qaramin ciki kada ta sha Quldul Hindiy.
Qusdul hindiy na iya tayar da hawan jini ko ya ta'azzara shi.
Kada a baiwa yara ƙanana Qusdul hindiy su sha.
Qusdul Hindiy na ainihin yana da yaji, in an bude shi ana yin Atishawa.
Daga shafin Bashir Halilu.
Lambar waya 08162600700.
Comments
Post a Comment