BINCIKEN ZAMANI AKAN YADDA AZUMI KE INGANTA LAFIYAR MUTANE. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

BINCIKEN ZAMANI AKAN YADDA AZUMI KE INGANTA LAFIYAR MUTANE.

Masu binciken na zamani su ka ce " Azumi, ko kuma barin cin abinci da shan wani abu na tsawon wani lokaci don neman lada ko inganta lafiya wani abu ne daɗaɗɗe sosai a duniya wanda wasu ke yinsa a al'adance wasu kuma a addinance. Yin hakan na da matuƙar amfani wajen  inganta lafiyar jiki da kyautatata". 
    Su ka ce "Binciken kimiyya wato 'science' ya hasko wasu fa'idoji da ke tattare da yin Azumi kamar haka:

1- Ciwon suga ko 'type 2 diabetes'. 
  Yin Azumi ko barin cin abinci zuwa wani lokaci
na taimakawa wajen daidaita suga da ke cikin jini ta hanyar ƙarfafa 'insulin' wanda ke taimakawa wajen tafiyar da 'glucose' yadda ya kamata, wanda hakan ke rage haɗarin 'type2 diabetes. 

2. Kumburin Jiki. 
     Mummunan Kumburin jiki na iya alaƙa da 
ciwon zuciya, cancer da amosanin gaɓɓai.      Bincike ya tabbatar da cewa Azumi na rage abubuwan da ke haifar da kumburin jiki tare da samar da ingantacciyar lafiya.

3. Rage ƙiba. 
  Azumi, musamman wanda wata rana ake yi, wata rana ana hutawa (kamar na nafila), yana taimakawa wajen rage ƙiba wadda tai wa mutum yawa da kuma sarrafa abinci da iska yadda ya kamata a jikin mutum. 

 4- Inganta aikin Ƙwaƙwalwa. 
   Azumi na inganta Ƙwaƙwalwa ta hanya ƙone guba da ƙwayoyin cuta daga cikin ƙwaƙwalwa tare da bayar da kyakkyawar gudunmawar lafiya ga ƙwaƙwalwa. 

5. Lafiyar Zuciya. 
      Azumi na rage kumburi tare da ƙarfafa hanyoyin sarrafa sugan da ke cikin jini ta yadda Azumin ke rage haɗarin kamuwa da ciwon zuciya. 
 

    6. Tsawon rai. 
       Masu binciken su ka ce suna ganin Azumi zai iya ƙarawa mutum tsawon rayuwa da daɗewa bai mutu ba saboda yadda yin Azumi ke da hanyoyin ƙara lafiya da kiyayeta masu yawan gaske. 

 7- Rigakafin Cutar Kansa (cancer). 
   Wani bincike ya nuna cewa yin Azumi ko baiwa ciki hutun cin abinci da shan ruwa, na kawar da abubuwan da ke sabbaba cutar kansa ajikin mutum. 

Lallai dai Azumi abu ne mai muhimmancin gaske wajen kyautata lafiyar mutum sannan ga samun lada idan mutum ya yi don Allah. 
 
    Ana bukatar wanda zai Azumi ya zama jikinsa zai iya ɗaukar Azumin sannan ya zama yana yinsa adadi da kuma yanayin da ba zai cutar da rayuwarsa ba, kamar yadda addini ya tsara. 

  Mai bukatar ya ga yadda waɗannan masana su ka yi wannan bincike sai ya duba waɗannan links da ke ƙasa:

(1) 8 Health Benefits of Fasting, Backed by Science. https://www.healthline.com/nutrition/fasting-benefits.

(2) Intermittent fasting: The positive news continues - Harvard Health. https://www.health.harvard.edu/blog/intermittent-fasting-surprising-update-2018062914156.

(3) Intermittent fasting: What are the benefits? - Mayo Clinic. https://www.mayoclinic.org/healthy-lifestyle/nutrition-and-healthy-eating/expert-answers/intermittent-fasting/faq-20441303.

(4) 11 Impressive Benefits of Fasting | Organic Facts. https://www.organicfacts.net/health-benefits/other/health-benefits-of-fasting.html.

Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

Comments

Popular Posts