YADDA AKW YIN MAN ALAIYADI. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846

YADDA AKE YIN MAN ALAYYADI. 

    Man Alayyadi ana yinsa ne da kwakwar da ke cikin ƙwallon kwakwar man ja. 
   Ana amfani da shi wajen girki, kayan ciye-ciye, gyaran jiki da kuma magunguna. 
   Za ka iya haɗa man Alayyadi da kanka a gida domin amfani da shi ko kuma yin na siyarwa. 

   Yadda za ka yi man Alayydi. 

  Da fari sai a samu ƙwallayen kwakwar man ja, a farfasa su, a fito da kwakwar da ke ciki. Sai a wanke kwakwar sosai, a cire datti. 
     A daka kwallayen nan ko a niƙa su, sai a zuba ruwa adadin yawan ƙwallon da aka daka (misali dakakken ƙwallo kofi biyu, to ruwan ma ya zama kofi biyu).
   A bar  ruwan aciki ya jiƙu tare da garin kwakwar, tsawon ƴan awanni, ko a bar shi ya kwana a jiƙe. 
      Daga nan sai a ɗora akan wuta a fara dafa shi, za a ga mai yana fitowa daga ciki. 
    Idan man ya gama fitowa sai a tace, a ware man daban. 

  Shi kenan an samu ingantaccen man Alayyadi mai kyau, mara haɗi, mara gurɓata.

    Ana amfani da Man Alayydi wajen gyaran fata, gyaran gashi kuma ana cin abinci da shi ko a sha shi a matsayin magani domin magance cututtuka da dama. 

   A shawarce kada mutum ya sha Man Alayyadi wanda bai tabbatar da inganci yadda aka haɗa shi ba.

   Idan kuna bukatar sani yadda ake amfani da Man Alayyadi sai ku yi magana in kawo muku.

  Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

Comments

Popular Posts