ADADIN RAKA'O'IN NAFILA DA MANZON ALLAH (SAW) YA KE YI ACIKIN DARE. Daga shafin Bashir Halilu.

ADADIN RAKA'O'IN NAFILA DA MANZON ALLAH (SAW) YA KE YI ACIKIN DARE. 
Manzon Allah (SAW) ya kasance yana sallah raka'a goma sha ɗaya ne, kamar yadda ya zo a ruwayar Bukhari da Muslim daga Nana A'isha (RA).
   Haka nan ya tabbata cewa wani lokacin Annabi (SAW) yana yin ƙasa da haka, wani lokacin kuma sama da haka.
    An samu ruwaya  dai daga Nana A'isha (RA) cewa wani sa'in Manzon Allah (SAW) yana tsayuwar dare da raka'a bakwai, wani sa'in kuma raka'a tara. 

An karɓo daga Zaidu bin Khalid Aljuhaniy cewa Manzon Allah (SAW) ya yi sallah raka'a goma sha uku acikin dare ɗaya. 

     Wasu Malami na ganin Annabi (SAW) ba a ruwaito ya yi raka'a sama da goma sha uku ba, don haka zai fi kyau mai nafila kada ya haura haka. Wasu kuma na ganin sallar nafila ba ta da iyaka, don haka mutum zai iya yai ta yi har yadda zai iya. 

    Allah Shi ne mafi sani. Allah Ya sa mu dace. 

فقد كان النبي صلى الله عليه وسلم يصلي إحدى عشرة ركعة، كما جاء في الصحيحين عن عائشة ـ رضي الله عنها ـ، وثبت أيضا أنه صلى الله عليه وسلم كان يقوم الليل بأقل منها، وبأكثر أحيانا؛ ففي البخاري عن عائشة ـ رضي الله عنها: أنه كان يقوم الليل بسبع وتسع. وعن زيد بن خالد الجهني أنه قال: لأرمقن صلاة رسول الله صلى الله عليه وسلم الليلة فصلى ركعتين خفيفتين ثم صلى ركعتين طويلتين طويلتين طويلتين ثم صلى ركعتين وهما دون اللتين قبلهما ثم صلى ركعتين وهما دون اللتين قبلهما ثم صلى ركعتين وهما دون اللتين قبلهما [ثم صلى ركعتين وهما دون اللتين قبلهما] ثم أوتر فذلك ثلاث عشرة ركعة. رواه مسلم.
والله أعلم. 

Comments

Popular Posts