BA A MUSU DA JAKI


Da Jaki da Damisa aka yi jayayya. Jaki ya ce "Ciyawa shuɗiya ce". Damisa ya ce "A'a, ciyawa koriya ce".

   Jaki ya kafe cewa lallai ciyawa shuɗiya ce, shi kuma Damisa ya dage cewa lallai ciyawa koriya ce. 

Da musu yay musu sai su ka ce "To a tafi wajen Sarki ya raba gardama".

  Sai su ka je wajen Zaki. Damisa shi ya fara magana. Ya ce "Ranka ya daɗe ni na ce ciyawa koriya ce amma Jaki ya dage cewa lallai ciyawa shuɗiya ce".

   Da jin haka sai Zaki ya ce "Jaki ya fi ka gaskiya" Sai ya yanke hukunci cewa a yiwa Damisa bulala kuma a ɗaure shi.

    Sai Damisa ya matso kusa da Zaki ya ce "Ranka ya daɗe, kai ma fa ka san cewa  ciyawar nan koriya ce amma ka baiwa Jaki gaskiya"

  Sai Zaki ya ce "To ai laifinka shi ne ka yi musu da Jaki. Wa ya gaya ma ka cewa ana musu da Jaki?".

Comments

Popular Posts