SIRRIN TURAREN WUTA KALA-KALA DA KAYAN HUMRA. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

SIRRIN TURARUKAN WUTA DA KAYAN HUMRA. 

Wadannan wadansu itatuwan bishiya ne da Allah madaukakin Sarki ya halitta a ban qasa. Wanda yin hayaqi da su ke da matuqar dadin qamshi da sakin zuciya da saka walwala. Musamman ga maza da mata.
Matan aure masu wayo ba sa sake wajen tanadarsu domin dadadawa megida rai.

Daga shafin Sunnah Medicine. Lambar waya 08162600700.

Yin amafani da irin wadannan itatuwa yana maganin Warin rima da kashe qwari da sanya daki tattausan qamshi, da kuma sanya nishadi ga mazauna dakin.

Ga wasu daga ciki

1- SANDAL:  Turare ne me kwantar da hankali. Saidai na ma'aurata ne domin yana motsa sha'awa.

 Idan mace tana turara dakinta da shi gefin magariba to ba qaramin riqe megidanta za dinga yi a gida ba. Kuma za ta qara shiga ransa. 
Akwai SANDAL Ja, akwai Fari,  akwai Baqi.

 Ana iya hada SANDAL da LUBBAN ZAKAR domin mayarda mamiji me kwadayi, Sai ki dinga turara shi a dakin.

2- AL'UL:  Turare ne mai dogon tarihi. Yin hayaqi da shi yana sa annashuwa. musamman idan an hada shi da ZUMA ana hayaqinsa. Yana qara danqon qauna ga ma'aurata.

3- GAF-GAF:  Wannan turare yana da muhimmanci sosai. Mace mai JINNUL ASHIQ wato Aljanin soyayya in tana amfani da shi insha Allahu zai gudu ya bar ta. Haka matar da ta dade ba tai aure ba. 

 Kuma yana maganin faduwar gaba, yawan ciwon mara, ciwon kai akai-akai, mafarkin mamijin dare dadai sauransu.

 Ana iya hada GAF-GAF  da HOGO ai hayaqinsu domin kara masa qarfi da ma'ana.

4- AMARIYA:  Wannan turare ne da Ma'aurata suke amfani da shi, domin yana da dadin qamshi da wanzar da soyayya. Yawan shafa shi ya kan sa ma'aurata yawan tina junansu.

5- HAWI: Wannan wani mashahurin itace ne da ake samunsa a Fakistan. Ana hada turarurruka da shi. Musamman wadanda suka shafi kwantar da hankali da nishadi. Ana ma hada Farar Humra da shi. Yin hayaqi da Hawiy yana kawo hira mai dadi a tsakanin ma'aurata.

  Ana iya hada HAWIY da RAIHATUL HUBBI da  SUZAN domin qara masa qarfi da fa'ida.

6- SINARIYO:  Ana yin turaren shafawa da shi domin daukar hankalin masoya. Yana kuma qara danqon zumunci.

 Yin amfani da shi yana riqe masoyi sosai.

 Ana iya hada SINARIYO da JAN AMBAR da MAHLABIYYAH da KAHLIJ da LAKOM da SIKE domin bayar da fa'ida ta musamman.

Wadannan turarurruka ne na MATAN AURE, iyayen gida da Amare.

   
 A fitowa ta gaba zan yi bayanin yadda ake hada Humra kala-kala. Irin su

1- Humrar ALADIN 
2- DORUT fari da ja.
3-DULKA
4-ELFASO 
.  Dadai sauransu insha Allah.

Daga shafin Sunnah Medicine. 
08162600700, 08134434846. 

Comments

Popular Posts