MAGANIN CUTAR HIV WATO QANJAMAU Na Gargajiya. Daga cibiyar Sunnah Medicine, masu harhada magunguna na Musulunci. http://www.facebook.com/sunnahmedicinepage/ Lambar waya 08162600700. Cutar HIV ita ce take zama AIDS kuma tana yakar garkuwar jiki mai kare mu daga cututtuka, wato tamkar tana yaki da sojojin da ke baiwa jikinka kariya, domin baiwa kowane irin makiyinka damar saurin hallakaka, ta hanyar cututtuka. ALAMOMIN KAMUWA DA CUTAR HIV. Idan kana fama da mafi yawan wadannan alamomi, to yana da kyau ka je ayi maka gwajin cutar. 1. Zazzabi da yaki ci yaki cinyewa; idan ana jin hakan har makonni bayan shan magani, a je ayi tes na cutar kanjamau. 2. Ciwon makoshi, wanda ake kira 'sore throat', idan ya hadu da sauran alamu, a binciki lafiya. 3. Kurarraji a fata. 4. Gumin dare bayan mutum na cikin ni'ima, kamar 'AC' ko fanka. 5. Kaluluwa. 6. Yawan ciwon jiki da gabobi. 7. Gajiya da raki, bayan ba'a yi aikin komai ba. 8. Barkewar zawo. 9. Yawan ciwon k...