AMFANIN DABINO GA MAI AZUMI. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

AMFANIN DABINO GA MAI AZUMI. 

Cin dabino lokacin da mutum ke jin yunwa, kamar lokacin da aka buɗe bakin Azumi ko kuma lokacin da aka tashi daga barci kafin a ci abinci yana da matuƙar amfani da ƙara lafiya ga al'uma. 

1- Kashe tsutsar ciki. 
    Cin dabino lokacin da ake jin yunwa, na taimakawa wajen kashe tsutsoci ci_ma_zaune da ke rayuwa acikin hanjin ɗan'Adam waɗanda ake kira 'Intestine worms". 

2- Ƙarfafa zuciya.  
   Cin Dabino lokacin da cikin mutum babu abinci na baiwa tsokar zuciya kuzari da aiki kamar yadda ya kamata.

3-Tsaftace hanta.
   Cin Dabino kafin a ci komai na wanke tsokar hanta da tsaftace ta. 

4- Samar da sinadaran jini. 
    Sinadaran 'iron' da 'vitamin C' da 'B5' da ke cikin Dabino na taimakawa wajen ƙara yawan jini ajikin mutum lokacin da ya zama dabino ya fara ci lokacin da ya ke jin yunwa kafin ya ci komai. 

5- Samar da Kuzari nan take. 
      Dabino na saurin samar da kuzari ga wanda ya tashi daga rashin lafiya ko matar da ta haihu ko kuma wanda yunwa ta galabaita shi.

6- Karkacewar baki ko wani ɓangare na fuska. 
    Cin dabino kafin a ci komai na taimakawa wajen dawo da jijiyoyin fuska da suka dena aiki. (paralyse of the facial nerve). 

 7- Ɗauke yunwa. 
   Cin Dabino kafin a ci komai na sa mutum ya wuni a ƙoshe ko kuma hana jin matsananciyar yunwa. 

 8- Samar da lafiyar fata. 
   Dabino ɗauke yake da sinadaran gina jiki kamar 'vitamin C' da vitamin 'B5' masu  samar da jini da kula da lafiyar jini da kuma sinadaran kashe dafi ko magance guba. Haɗuwar waɗannan sinadarai na samar da lafiyayyiyar fata ga mutum da magance cututtukan fata da sanya fatar jiki ta yi kyau. 

   9- Samar da lafiyayyen gashi mai kyau. 
   Wasu sinadarai da ke cikin dabino kamar
'vitamin B5' da ' iron' suna taimakawa wajen tsiro da gashi da kuma samar da lafiyayyen gashi mai kyau musamman idan ana fara cin dabino kafin a ci komai. 

  10- Maganin Amosani. 
  Haka nan dabino na taimakawa wajen gudanar jini a fatar kai, wanda hakan ke magance amosani da zubewar gashi.

11- Daidaita kitse a jikin mutum. 
   Bincike ya nuna Dabino na taimakawa wajen rage damuwa da daidaita kitse a jikin mutum musamman idan ana cinsa kafin a ci komai saboda sinadaran 'fiber da 'iron' da ke cikinsa. 

Masana lafiya na ba da shawara cewa ya kamata dabino ya zama yana cikin abinda mutum ke ci kullum da safe kafin karyawa ko kuma lokacin da cikin mutum babu abinci, kamar lokacin buɗa bakin Azumi.

  Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

Comments

Popular Posts