AMFANIN ZAITUN
AMFANIN ZAITUN GA DAN'ADAM Daga shafin Magunguna a Musulunci. https://www.facebook.com/groups/842715785785303/ Lambar waya 08162600700. Amfanin zaitun a jikin ɗan Adam wanda ya kamata mu sani, Shi dai zaitun itaciya ce mai albarka da kuma ba da cikakkiyar lafiya a jikin ɗan Adam, kamar yadda muka sani cewa, zaitun abu ne mai daraja, kamar yadda muka samu bayaninsa a cikin ALKUR’ANI MAI GIRMA haka kuma kamar yadda aka samu daga hadisan Manzon Allah (S.A.W) An karɓo daga sayyadina Umar yana cewa Manzon Allah (S.A.W) ya ce ku yi abinci da man zaitun kuma ku shafa shi a jikinku, domin haƙiƙa shi yana daga a cikin bishiya mai albarka. tirmizi ne ya rawaito Daga Cikin aikin da man zaitun yake a jiki CIWON CIKI Duk mutumin da yake ciwon ciki, sai ya samu man zaitun kamar cikin cokali, ya hada da garin habbatussauda ya cakuɗa, ya sha safe da yamma. Ya samu kamar sati ɗaya yana sha ko kina sha, insha Allah zai samu lafiya. CIWON KAI Duk mutumin da yake ciwon kai, to sai ya samu man zaitun,...