ƘISSAR AL'HUD'HUDA DA ANNABI SULAIMAN (AS).
Daga Shafin Bashir Halilu. Wata rana Annabi Sulaiman عليه السلام ya fita zuwa wata tafiya shi da jama'arsa, sai ya kasance rana ta yi tsananin zafi. Sai Al'hud'huda su ka zo su ka buɗe fuka-fukansu a sararin samaniya, su kay wa Annabi Sulaiman عليه السلام rumfa, har ya zamanto ya samu inuwa. Sai Annabi Sulaiman (AS) ya ji daɗin abinda su kay masa. Ya ce musu "Me ku ke so nay muku kyauta da shi?" Sai babbansu ya ce "Mu na so kowanne a cikin mu a saka masa kambun zinare a tsakiyar kansa. (Wato hular sarauta ta zinare)". Sai sauran Alhud'hudan su ka ruɗe "E muna so, e muna so, kowannenmu yana buƙatar hular zinare". Sai Annabi Sulaiman (AS) ya roƙi Allah Ya fito musu da hular zinare akansu, sai kuwa kowanne ta fito masa. Sannan Annabi Sulaiman (AS) ya ce musu "Wannan hular Zinaren sai ta zama fitina a kanku". Daga nan sai Alhud'huda su ka ...