AMFANIN SHAN RUWA YAYIN BUƊA BAKI. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

AMFANIN  SHAN RUWA LOKACIN ƁUDA BAKI

Manzon Allah (SAW) ya yi umarni ga mai Azumi cewa ya yi buɗa baki da dabino, wato ya fara cin dabino lokacin da ya kai Azuminsa, sai ya ce wanda bai samu dabino ba ya fara da shan ruwa domin shi ruwa abu ne mai tsarki. 

   Bayan mun yi bayani akan yadda cin dabino lokacin buɗa baki ke da muhimmanci wajen kyautata lafiyar ɗan-Adam yanzu kuma za mu yi bayani akan amfanin shan ruwa kafin a ci komai, wato lokacin Buɗa baki. 

YADDA SHAN RUWA LOKACIN BUƊA BAKI KE KYAUTATA LAFIYAR ƊAN ADAM. 

      1- Wanke hanji da tsaftace shi. 
    Shan ruwa lokacin buɗa baki  yana taimakawa wajen wanke dattin da ke cikin hanji, ya ƙarfafa motsin hanji kuma ya taimakawa gaɓoɓin da ke narka abinci da sarrafa shi a jikin mutum. 

   2- Fitar da guba. 
    Shan ruwa kafin a ci komai yana wanko guba da ke cikin ciki kuma ya fitar da ita. Hakan na ƙarawa mutum kyawun fatar jiki da hasken fuska.

   3- Magance ciwon kai. 
     Rashin ruwa a jiki babban sanadi ne na samuwar ciwon kai, Shan ruwa kafin a ci komai bayan magance ciwon kai da ya ke yi yana ma inganta hanyoyin numfashi da kuma ƙara lafiyar haƙora. 

4- Buɗe ciki domin cin abinci. 
   Shan ruwa yayin buɗa baki ko kafin a ci komai yana wanke abinda yai ragowa acikin mutum sannan ya buɗe hanyar jin yunwa, wanda hakan za taimakawa mutum ya samu cin abinci sosai. 

      5- Ƙara kuzari. 
      Shan ruwa lokacin buɗa baki na taimakawa wajen samarda wani sinadarin jini da ake kira 'red blood cells'  wanda ke taimakawa wajen samar da ƙarfi ko kuzari a jikin mutum. 

    6- Ƙara kuzarin ayyukan jikin mutum. 
   Shan ruwa kafin a ci komai yana ƙarfafa aikin jikin mutum wajen sarrafa abinci ya zama ɓangaren jiki da kuma fitar da mara amfani zuwa inda ya dace da kashi 25%. 

7- Rage nauyi. 
     Shan ruwa kafin a ci komai na taimakawa wajen rage nauyi ga mutanen da nauyin ƙibake damunsu, kasancewar ruwa ba shi da 'calories'. 
  
Kada dai a manta, shan ruwa abu ne mai muhimmanci wajen kyautata lafiya ko da lokacin buɗa baki ne ko kuma sauran lokuta. 

   Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

Comments

Popular Posts