Posts

Showing posts with the label sunnah medicinw

ASSARIMUL BATTAR

Image
Daga Littafin 'ASSARIMUL BATTAR' Malamai daga shafin Sunnah Medicine sun tattaro wasu alamomi da za ka iya gane cewa Aljani ya shafi mutum ko kuma an yi masa asiri domin ka taimaka ma sa .  1. Mutum ya zama ba ya son karatun Alkur'ani ko saurarensa  2. Rashin son yin ibada kamar sallah, ko a yi ta cikin bacin rai da kasala.  3. Yawan ciwon kai mai tsanani ko 6arin kai ko kuma jiri.  4. Yawan ciwon mara ko baya ko kwankwaso ko kuma ciki wanda ba ya jin magana kuma an rasa me ke kawo shi.  5. Yawan jin tafiyar wani abu a jiki kamar kiyashi ko tsutsa ko kwarkwata tana yawo a kai amma idan an duba ba za a ga komai ba.  6. Yawan mafarke mafarke na abun tsoro ko firgirta da surutai a cikin bacci ko kuma mutum ya ji wani abu mai nauyi ya danne shi ko ya shake masa wuya.  7. Yawan jin tsoro ko faduwar gaba ko wani abu ya dinga yi ma ka gizo ko kuma ka ji kamar ana kiran sunan ki amma ba za ka mai kiran ba. 8. Yawan jin sanyi ko zafi ko rikewar kafa ko wani sas...