AMFANIN TUFA (APPLE). Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
AMFANIN TUFFAH (APPLE)
Tuffa 'yar itaciya ce mai muhimmanci sosai ga lafiyar al'umma.
Daga cikin amfaninta, tana:
★Kyautata Lafiyar Hakora da saka su Haske.
Tauna Tufa yana rage kwayoyin cuta dake kama hakora. Yana kuma maganin ru6ewar hakora tare da saka su haske.
.
.
★Saukaka Tauna Abinci.
Tufa tana samar da miyau a cikin baki. Wanda ke taimakawa wajen tauna abinci da hadiyarsa cikin sauqi tare da hana bushewar maqogwaro.
.
.
★Rigakafin Cutar Kansa (cancer).
Shan Tufa yana da kashi 23 bisa 100 na rage hadarin kamuwa da cutar kansa.
.
.
★Rage Hadarin Kamuwa da Cutar Deabetes.
Matan da suke cin Tufa aqalla guda daya a rana, suna da kariya 28 bisa 100 sama da wadanda basa ci, daga kamuwa da cutar deabetes type2.
.
.
★Rage Kitse.
Tufa tana da sinadaran da ke rage kitse daga cikin hanjin mutum tare da samar masa da ingantacciyar lafiya.
.
.
★Lafiyar Zuciya.
A cikin musamman Fatar Tufa, da akwai sinadaran da ke daidaita shige da ficen jini a cikin zuciya tare da ba ta ingantacciyar lafiya.
.
.
★Maganin Ciwon Kai.
A feraye Tufa a ci banda 6awon yana taimakawa sosai wajen maganin ciwon kai.
.
.
★Cushewar Ciki.
Shan Tufa hade da Zuma yana maganin cushewar ciki da ke hana cin abinci.
Daga shafin Bashir Halilu.
WhatsApp 08162600700, 08134434846.
Comments
Post a Comment