ƘISSAR ANNABI AYYUBA (AS). Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
ƘISSAR ANNABI AYYUBA ALAIHIS SALAM
Allah Ubangiji Sub'hanaHu wa Ta'ala Ya za6i Annabi Ayyuba (AS) da Annabta, kuma Ya yalwata masa duniya sannan ya kasance yana da duk wani nau'i na dukiya na daga Rakuma da Shanu da kuma sauran dabbobi da dawaki sannan ba wani mutum da ya kaishi yawan dukiya a wannan lokacin kuma Allah Ya hore masa 'ya'ya maza da mata.
Annabi Ayyuba (AS) ya kasance mutum ne mai yawan tsoron Allah (SWT) sannan mai yawan tausayawa talakawa da Miskinai da daukar dawiniyar marasa aure mata da maza kai harma da Marayu. Annabi Ayyuba mutum ne mai taimakawa baqi da matafiya sannan ya kasance mai yawan godeWa Allah akan ni'imomin da Ya yi masa sannan kuma mai kokarin sauke haqqin da ke kansa ne.
• A can sama kuwa, Mala'iku sun kasance kullum suna ambaton ayyukan alkahairin Annabi Ayyuba (AS), tare da ambaton kyawawan halayensa kuma suna yi masa salati. A kullum Ambatonsa karuwa yakeyi a wajensu, saboda yadda ake hawowa da ayyukansa kyawawa zuwa sama. Haka abin yake kamar yadda ya zo a Hadisi cewa idan Allah Madaukakin Sarki yana son Bawa, sai ya kira Mala'ika Jibriliu ya ce masa, Ya kai Jibrilu, Hakika Ni ina son wane, kai ma ka so shi, Daga nan sai Mala'ika Jibrilu yay shela acikin Mala'iku cewa Allah Yana son wane, ku ma ku so shi. Sai ambatonsa ya cika sama, dukkan Mala'iku su dinga sonsa tare da yi masa addu'a. Don haka ne ambaton Annabi Ayyuba (AS) ya cika sama, domin a lokacin babu mutumin kirki kamarsa a duniya.
• Shi kuwa Iblis La'anatUllahi alaihi, ya kasance a lokacin ba a hana shi hawa sama ba amma bayan aiko Annabi Muhammad SallAllahu alaihi wa sallam, an hana Iblis hawa sama kwata-kwata. To a wancan lokacin na Annabi Ayyuba (AS), a duk lokacin da Shaidan ya hau sama sai ya ji Mala'iku suna ta yabon Annabi Ayyuba (AS), tare da fadar ayyukan alkhairinsa. Wannan sai yasa hassada ta kama Shaidan kuma ya fara tunanin yadda zai yi ya hana Annabi Ayyuba (AS) aikata wannan biyayya da yakewa Allah Madaukakin Sarki.
Wata rana sai Shaidan La'ananne ya ce "Ya Ubangiji, na yi nazari akan BawanKa Ayyuba, sai na ga Ka yi masa ni'ima, shi kuma sai ya gode maKa sannan dukkan abinda Ka ba shi na umarni yana aikatawa, sannan Ka ba shi lafiya, sai ya gode maKa. To ai baKa ta6a jarrabarsa da wani tsanani ba, na tabbatar da za Ka jarrabe shi da wani bala'i to da butulce maKa zai yi kuma ya manta da Kai".
Bayan Shaidan ya gama wannan bayani na sa, sai Allah Madaukakin SArki Ya ce masa " Je ka, Na baka dama akan dukiyarsa".
Da Shaidan ya ji haka, sai ya je ya tattara ma'abotansa ya shaida musu cewa an ba shi dama akan dukiyar Annabi Annabi (AS) amma me suke da shi na karfi ko dabara?!. Sannan ya shaida musu cewa gushewar dukiya ba karamar musiba bace ga mai ita, sannan musiba ce wacce mutane basa iya hakuri akanta, don haka suna ganin wannan wata babbar dama ce suka samu domin jefa Annabi Ayyuba (AS) acikin hallaka.
Da jin haka sai wani Shaidani ya ce "Ni an bani wani karfi da nake iya tada guguwa da shi (a ilimin ANWA'UL JINNI ana kiran irin wannan Aljani mai tada guguwa da suna Jiinul Ghubar, na yi cikakkken bayaninsu a shafina) ya ce da zaka yarda, da sai in je na tada wata iska mai karfi tare da wuta, ta kone dukkan abinda Annabi Ayyuba ya mallaka. Sai kuwa Shaidan ya ba shi dama. Sai ya tafi, ya tada guguwa tare da gobara, wuta ta kama dukiyar Annabi Ayyuba (AS) tare da dabbobinsa. A lokacin da wutar ta kama mutanen gari suna kallo amma ba mai iya tunkarar wutar saboda bala'in karfinta, haka kowa ya tsaya, ya zubawa Sarautar Allah ido, har wannan wutar ta kone dukiyar gabadaya. (su ma Aljanu masu kunnawa kayan mutane wuta ana kiransu Jinnun Nariy, za ka iya samun cikakken bayani akansu alambarmu ta whatsApp, 08162600700)
Da Shaidan yaga haka, sai yayi shiga, irinta mai yiwa Annabi Ayyuba (AS) hidima, ya je ya tarar da Annabi Ayyuba (AS) yana sallah, da ya idar sai ya ce masa " Ya Ayyuba, shin ka san abinda Ubangijin da kake bautawa ya aikatawa dukiyarka kuwa?". SAi ya ce "Me Ubangijina Ya aikata?". Sai ya ce "Ai duk ya qone maka ita". Da Annabi Ayyuba (AS) ya ji haka, sai ya ce "To ai dama dukiyar ta Allah ce, ni aro ya bani, domin in kula maSa da ita, na aikata maSa abinda Ya ke so da ita, yanzu kuma Ya kar6i ajjiyarsa, don haka ina gode maSa, domin na kara samun cikakken lokacin da zan ta bautar Allah".
Su kuwa mutanen gari suna ta cewa "Ai da alama dai Ayyuba ya sa6i Ubangijinsa, in ba haka ba ba Zai aiko wuta lokaci guda ta cinye masa dukiya haka ba, su ka ce lallai da alama Ubangijin Ayyuba Ya yi fushi da shi amma shi kuwa Annabi Ayyuba (AS) yana ta nuna musu cewa wannan ba komai bane face jarrabawa daga Allah, da Yake yiwa bayinSa domin Ya ga ko zauyi maSa godiya kokuma zasu butulce maSa.
Lokacin da Shaidan ya koma sama, sai ya ji ambaton Annabi Ayyuba (AS) ya karu a bakin Mala'iku, suna ta hirar irin jarrabawar da Allah Yay masa da kuma, yadda ya ci jarrabawar, don haka suna ta yabonsa da kuma yi masa salati. Wannan tasa baqin ciki da takaici suka cika zuciyar Shaidan, ransa ya 6aci, ya ce "Ya Ubangiji, ai don ka baiwa Ayyuba 'ya'ya ne, da zaka kar6e 'ya'yan da ka ba shi, ai da ba zai iya hakuri ba". Sai aka ce an ba shi dama akan 'ya'yan nasa, don haka Shaidan ya tafi da gayyarsa, suka turowa 'ya'yan Annabi Ayuuba (AS) katanga akansu a lokacin da suke bacci, dukkansu suka mutu a lokacin. Sai kuma ya canja siffarsa kamar wani Malami, masanin hikima, ya sanya rawani akansa da fuskarsa, ga kuma jini yana malala a fuskarsa, sannan ya tafi wajensa, ya ce "Ya Ayyuba, shin ka ga yadda aka azabtarda 'ya'yanka kuwa, aka turo musu gini suna kwanance, kawunansu su ka farfashe, suna ta zubar jini? kuma da ka ga yadda aka farke cikinsu, kayan cikinsu su ka firfito, na tabbatar da ba za ka ji dadi ba. Shaidan ya ci gaba da gayawa Annabi Ayyuba (AS) abin tausayi da ya faru ga 'ya'yansa, har saida ta kai ga Annabi Ayyuba (AS) ya zubar da hawaye saboda tausayi. Da ganin haka sai Shaidan ya fita yana mai farin ciki da murna, yana gaggawa zai hau sama, domin yana ganin ya ci nasara akan Annabi Ayyuba (AS), domin ya sa shi ya zubar da hawaye.
Shi kuwa Annabi Ayyuba nan take sai ya tuba ga Allah kuma ya gode maSa kan ni'imomin da Yay masa.
Lokacinda Shaidan ya hau sama, sai ya ji yabon da akewa Annabi Ayyuba (AS) ya fi na kullum ma, Mala'iku suna fadin kokarinsa akan hakurinda yay na rashin dukiya da `ya`ya da kuma yadda yake saurin mika al'amuransa zuwa ga Allah Madaukakin Sarki. Da Shaidan ya ji haka sai zuciyarsa ta dugunzuma, takaici da kunya suka lullu6e shi, sai ya bude baki yana mai asara kuma ta6a66e, ya ce " Ya Ubangiji, ai don Ayyuba ya ga ka barshi da lafiyarsa ne, da zaka jarrabeshi da cuta ai da ba zai iya jurewa ba. Matukar ka kar6e lafiyar daka ba shi to bijire maka zai yi. Sai aka ce to an ba shi dama akan gangar jikin Annabi Ayyuba (AS) amma banda harshensa da hankalinsa da kuma zuciyarsa, domin Shaidan ba ya iya shiga zuciyar Annabawa Alaihimus salam ko ya ta6a hankalinsun ko ya sanya musu wani abu akan harshensu. https://t.me/tarbiyyahislamiyyah/14
*AN JARRABI ANNABI AYYUBA ALAIHIS SALAM DA CUTA*
Fadin Allah Madaukakin Sarki, acikin Alqur'ani:-
بسم الله الرحمن الرحيم
وَاذْكُرْ عَبْدَنَا أَيُّوبَ إِذْ نَادَىٰ رَبَّهُ أَنِّي مَسَّنِيَ الشَّيْطَانُ بِنُصْبٍ وَعَذَابٍ (41) .
Ma'ana
_"Kuma ka ambaci BawanMu Ayyuba a lokacin da ya kirayi Ubangijinsa, (ya ce) Hakika ni Shaidan ya shafeni da wahala da kuma wata cuta"_.
Nan da nan sai Shaidan La'ananne ya tafi wajen Annabi Ayyuba (AS) ya sameshi yana sallah, ya yi sujjada, sai Shaidan yay kokarin dago kansa amma ya kasa, ya rasa yadda zai yi. Sai ya zo masa ta karkashin qasa daidai inda yay sujjadar, domin yay masa busa acikin hancinsa, ya je masa ta qasan diddigensa, ya shiga cikin jikinsa, har cikin 6argonsa, ya sa masa wata cuta da ciwon jiki, ta inda miki zai fito daga nan sai wannan ciwo ya bayyana a gare shi, har ta kai mutane sun fara gudunsa, in banda matarsa kadai, ita ce kawai ba ta guje shi ba, wacce aka ce jikar Annabi Yusuf ce Alaihis salam, dan Annabi Ya'aquba Alahis salam.
Ita wannan mata ta sa ta kasance tana matukar lura da shi kuma tana girmama shi, yadda ya kamata.
Ganin tsananin cuta da yake ciki da kuma yadda mutane suka guje shi, yasa wasu mutum uku da sukayi imani da shi suka ziyarce shi, su ka ce "Ya Annabin Allah, ya kamata ka nemi gafarar Ubangijinka akan zunubin da ka aikata maSa, Yake azabtar da kai haka, Ya halakar maka da dukiya da kuma 'ya'ya.
A lokacin ne Annabi Ayyuba (AS) yay musu wata nasiha mai tsawo, mai ratsa zuciya wadda ta kunshi kalmomin tauhidi da mika al'amura ga Allah da hakuri da kuma juriya akan musiba sannan ya fadakar da su cewa mutum ba ya samun daukaka da matsayi awajen Allah sai bayan ya fuskanci jarrabawa irin wannan ko makamanciyarta daga wajen Allah Madaukakin Sarki kuma yayi hakuri. Hakanan ya nuna musu cewa ba wai sai lallai mutum ya aikata sa6o sannan Allah yake jarrbarsa da cuta ko rasa dukiya ba, a karshe dai ya ce shi yana mai mika lamarinsa ga Allah, domin Shi Ya jarrabeshi kuma Zai yaye masa. Annabi Ayyuba (AS) ya kara musu da cewa, "Kun zo min, kuna kuka, tun kafin a dake ku, kun tsorata tun kafin a tsorata ku, ni ban nemi wani acikinku yay sadaka da dukiyarsa ko ya nemi kusanci da wani abu da yake da shi don a yaye min abinda yake damuna ba. Ku yanzu kuna ganin kamar biyayyar da kuke yiwa Allah ce ta sa Allah bai jarrabeku ba?!. To ai yanzu da Allah Zai bude muku abinda yake tsakaninku da Shi, da sai ku ga kuna da wadansu laifuka da Ya 6oye muku kuma Ya ba ku lafiya. Don haka ma ni a yau kun fi zamar min tsanani fiye da cutar da take damuna.
Daga nan sai ya kaurace musu, ya fuskanci Ubangiji, yana mai tuba da neman gafara, yana qasqantar da kai, yana yabaWa Allah akan ni'imomin da Ya yi masa, yana mai kai kukansa zuwa ga Allah Mai girma da daukaka, yana cewa " Ya Ubangiji, ga BawanKa mai rauni, na samu kaina acikin jarrabarda ko Rakumi aka dorawa ba zai iya daukarta ba, yatsuna sun yayyanke, bana iya daukar wani abinci zuwa bakina, sai da matukar wahala. Ya Ubangiji, naman kaina ya zagwanye, ba wani nama a tsakanin kunnuwana guda biyu sannan kuma gashin fuskata duk ya zube, kamar an kone fuskata da wuta sannan idanuwana suna reto tsakanin kundukukina, ga harshena ya zazzago, ya cika bakina, le6ena ya zazzago, ya rufe saman hancina da kasan ha6ata, kayan cikina duk sun yayyanke, domin in na shigar da abinci cikina haka yake fita kamar yadda na shigar da shi, ba ya amfana min komai. Ga karfina ya tafi, kafafuwana kuma sun bushe, ba ni da ikon daga su, dukiyata ta tafi, wanda nake daukar nauyinsa ya zamto shi ne wanda yake ba ni loma daya, shi ma yana mai min gori da wulakanci akanta. Ya Ubangiji, 'ya'yana sun hallaka, 'yan uwana duk sun gujeni, abokaina ma duk sun gujeni, na rasa ma'aikata, ina ta raki babu wanda zai tayani, uzurai sun yawaita akaiana, na kira mai yi min hidima bai amsa min ba, na rasa hakkokina da suke wajen abokaina. Ya Ubangiji, hakika karfin mulkinKa shi ne ya sa mun rashin lafiya ya raunana jikina, da dai ace Ubangijina zai sakar min harshena da na yi magana duk da cewa bakina ya cika. t.me/tarbiyyahislamiyyah
*UBANGIJI YA YAYEWA ANNABI AYYUBA ALAIHISSALAM CUTA.*
Lokacin da Annabi Ayyuba (AS) ya gama wannan jawabi ga wadannan mutane da su ka ziyarceshi, sai ya cigaba da kaskantar da kai ga Allah madaukin Sarki tare da neman taimakonSa akan Ya yaye masa abinda ke damunsa. Nan take sai su ka ga wani girgije ya lullu6esu, har saida su ka zaci cewa wata azaba ce ta daban, sai aka yi wani kira da cewa "Ya Ayyuba, hakika Ubangijinka yana cewa ga ni nan a kusa dakai, dama kuma ban gushe ba ina tare da kai. Don haka tashi ka mike tsaye, ka daidaita tsayuwarka, kuma kayi magana da harshenka.
Haka dai aka ci gaba da gayawa Annabi Ayyuba (AS) kalmomi na Tauhidi, masu kara nuna giman Allah Madaukakin Sarki tare da karfin mulkinSa da kuma tabbatar da cewa komai a hannun Allah yake, Shi ke juya shi yadda Ya so.
Sai Allah Mai girma da daukakaka Ya ce da shi "Ya Ayyuba, Mun jefa hukuncinMu a gareka kuma dama rahmaTa ta rigayi uqubaTa idanma har ka yi kuskure, to hakika Na gafarta maka abinda ka fada kuma na yi maka rahma sannan kuma Na dawo maka da ahlinka da dukiyarka da kuma wadansu kwatankwacinsu, domin ya kasance abin izna ga wadanda suke bayanka sannan ya zama abin izna da lura ga wadanda aka jarraba da kuma gaisuwa ga masu hakuri.
Sai kuma Allah Madaukakin Sarki ya ce masa :-
ارْكُضْ بِرِجْلِكَ ۖ هَٰذَا مُغْتَسَلٌ بَارِدٌ وَشَرَابٌ (42)
Ma'ana
_"Doki qasa da sawun (qafar) ka, wannan abin wanka ne, mai sanyi da kuma sha"._
Sai kuwa Annabi Ayyuba (AS) ya daki kasa da sawun kafarsa, nan take sai ruwa ya 6u66ugo daga kasa, sai yayi wanka da wannan ruwa kuma ya sha daga gareshi. Sai dukkan cutar da ke jikinsa ta filin data 6oye ta warke.
To bayan ya gama wanka da ruwan, dukkan cutar da ke jikinsa ta kau, sai ya samu guri ya zauna, a lokacin matarsa bata nan. Lokacin data dawo sai ta fuskanto shi, take tambayarsa da cewa "Kai Bawan Alllah, shin ko ka san wanda aka jarraba wanda yake zaune anan?". Sai ya ce "Shin ko za ki ganeshi idan kika gan shi?". Sai ta ce "Na'am, ta yaya ba zan gane shi ba?!". A lokacin da yay murmushi sai ta gane shi, sai ta sunbace shi.
Ibn Abbas Allah Ya kara yarda agareshi, yana cewa "Na rantse da Wanda raina yake hannunSa, bata gama sumbatarsa ba, sai ga shi an dawo masa da dukkan abinda ya mallaka, na duikya da 'ya'ya.
Wasu Malaman tarihi ma su kace, `ya`yan nasa aka dawowa da ransu, dukkansu su ka tashi, hakama dukiyarsa da dabbobinsa, anan take aka dawo masa da su sannan Allah Ya ninka masa komai nasa.
Shi ne inda Allah Madaukanin Sarki Yake cewa acikin Alqur'ani mai girma:-
وَأَيُّوبَ إِذْ نَادَىٰ رَبَّهُ أَنِّي مَسَّنِيَ الضُّرُّ وَأَنتَ أَرْحَمُ الرَّاحِمِينَ (83) فَاسْتَجَبْنَا لَهُ فَكَشَفْنَا مَا بِهِ مِن ضُرٍّ ۖ وَآتَيْنَاهُ أَهْلَهُ وَمِثْلَهُم مَّعَهُمْ رَحْمَةً مِّنْ عِندِنَا وَذِكْرَىٰ لِلْعَابِدِينَ(84)
Ma'ana:-
"Ambaci Ayyuba, alokacin da yake rokon Ubanginsa, (yana mai cewa) hakika ni tsanani ya sameni kuma Kaine Mafi jin qan masu jin qai. sai Mu ka amsa masa rokonsa kuma Mu ka yaye masa abinda yake tare da shi na daga tsanani, Mu ka ba shi iyalinSa kuma Mu ka kara masa misalinsu tare da su, don jin qai daga garemu da gargadi ga masu bauta".
(Suratul Anbiya'i, ayah ta 82 zuwa ta 83).
*Wasu daga cikin darusan da za mu iya dauka a wannan Qissa.*
1- Yadda Mala'iku suke yabo tare da ambaton masu aikata alkhairi.
2- Da farko Shaidan yana iya hawa sama amma daga baya an hana shi.
3- Irin tsananin kiyayya da gabar da Shaidan yakeyi ga Bayin Allah na_gari.
4- Shaidanu suna iya kunnawa kayan mutane wuta.
5- Shaidanu kan iya sakawa mutum rashin lafiya ajikinsa.
6- Yadda Annabawan Allah su ke iya jure jarrabawa komai tsananinta.
7- Komai tsananin ciwo in an yi hakuri Allah Yana da maganinsa.
Da dai darussa da yawa. Allah Ya sa mu dace.
Daga shafin Bashir Halilu Tarbiyyah Islamiyyah, mai ruq'yah da harhada magungunan Musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
Comments
Post a Comment