Posts

Showing posts with the label ƙissa labarai kissoshin Annbawa

YADDA IBLIS YA SO YA ƁATAR DA MATAR ANNABI AYYUBA (AS).

Image
   Daga shafin Bashir Halilu.     Mun karanta a ƙissar Annabi Ayyuba (AS) cewa Allah Ya jarrabe shi da rashin lafiya mai tsanani, wacce ta kai ba ya iya komai da jikinsa, ƴaƴansa duka su ka mutu, dabbobinsa duka su ka mutu, dukiyarsa ta ƙare, jama'arsa su ka guje shi, sai matarsa ce kawai ta kasance tare da shi ta ke taimakonsa. Ita ce mai nemo abinci da gyara masa jikinsa. Kafin rashin lafiyar, Allah Ya azurta Annabi Ayyuba da yawan ƴaƴa da tarin dukiya mai yawa da ma'aikata da manyan gine-gine da taimakon mabuƙata da yawan ibada, kamar dai yadda mu ka kawo a cikin ƘISSAR ANNABI AYYUBA (AS).       Ibni Abid Dunya, ya kawo acikin littafinsa Maka'idish Shaiɗani cewa:      "Fudhayl bin Abdul-Wahhab ya ba mu labari, ya ce: Abubakar bin Ayyash ya ba mu labari, daga Ibn Wahb bin Munabbih, daga mahaifinsa, ya ce:       "Iblis ya tambayi matar Annabi Ayyuba (A.S), ya ce:      “Me ya sa kuka fuskanci wannan bala’in ...