Posts

Showing posts with the label jifa

SIHIRIN JIN MAGANGANU KO MURYOYIN MUTANE KUMA BA A GANINSU SIHRUL HAWATIF (سِحْرُ الْهَوَاتِفِ) Daga shafin Dr. Bashir Halilu. Lambar waya 08134434846.

Image
     A cikin rubutun Shaikh Waheed bin Abdus-Salam Baali, mai taken  «سحر الهواتف (أعراضه - كيف يحدث؟ - علاجه)»,  ya yi bayani a kan wannan nau'in sihiri da ake kira 'Sihrul Hawatif'      A  bayanin da wannan malami ya kawo, wannan nau'in sihiri yana saka mutum yawan mafarkai masu ban tsoro, jin muryoyin mutane suna maga kuma  ba a ganinsu, yawan wasuwasin zuciya da shakku a kan abokai da masoya. YADDA  ALAMOMIN SIHRUL HAWATIF SU KE. GA MUTUM.    Ga wasu alamomi da abubuwan da aka ambata a cikin bayanin Shaikh Waheed bin Abdus-Salam Baali, tare da ƙarin bayani domin sauƙin fahimta. 1- الْأَحْلَامُ الْمُفْزِعَةُ     Mafarkai masu ban tsoro.     Mutum ya dinga yawan yin mafarkai masu tayar da hankali, tsoratarwa ko firgici, har ya dinga tashi daga bacci cikin razana, wani ma yana zurawa da gudu ko ihu bayan ya farka. 2- سَمَاعُ مَنْ يُنَادِيهِ فِي الْمَنَامِ      Mutum ya dinga ...

ASIRIN HANA HAIHAUWA

ASIRIN HANA HAIHUWA Abu ne sananne cewa akan iya yiwa namiji ko mace sihiri,  domin ahana mutum haihuwa,  ko mace ta dinga yawan yin 6arin ciki,  da dai sauransu. A wannan lokaci za muyi bayani ne insha Allahu akan alamomin da mutum zai gane cewa matsalar haihuwarsa tana da alaqa ne da sihiri ko jinnu ko kuma ba ta da alaqa da su. Kafin nan,  ga wadansu dalilai na dabi'a,  wadanda suke hana daukar ciki,  koda kuwa babu asiri ko Aljani a tare da mutum. ABUBUWAN DA KE HANA SAMUN CIKI 1- ‘Kan‘kantar gaban namiji,  idan ya kasance ba ya iya kaiwa har bakin mahaifarta. 2- ‘Karancin ruwan namiji, ta yadda ba shi yawan da zai iya gangarawa har inda ake so ya je. 3- Fitar jinin haila mai yawan gaske,  wanda kan iya wanko abinda ke cikin mahaifar. 4- In mace tana rub-da-ciki bayan gama saduwa,  hakan zai sa dukkan abinda mijinta ya zuba mata ya dawo,  ba zai shiga mahaifarta ba. 7- Damuwa mai tsanani ko rashin kwanciyar...

BAYANI AKAN RAUHANAI Shin Rauhanay Aljanu ne ko Mala'iku?

Image
MENENE RAUHANIY ? Su waye Rauhanay ? . . _Wasu mutane suna ikirarin cewa suna aiki da Rauhanay,  inda suke taimaka musu wajen bada magani ko wasu ayyukansu na rayuwa.  To su waye rauhanay kuma aiki da su ya halarta?_ ```Daga cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah,  masu yin ruqiyyah da harhada magungunan musulunci.  Lambar waya +2348162600700, +2348134434846.``` . . بسم الله الرحمن الرحيم. Da farko dai kalmar *Rauhan* tana nufin wani 6oyayyen ilimi wanda  Allah Ya ke6anci wasu daga cikin bayinsa da shi,  in ba su ba ba wanda ya sanshi,  Allah ne yake za6ar wasu daga cikin bayinsa Ya sanar da su. Kenan kalmar _Rauhaniy_ tana nufin _wanda yake da ilimin da kowa bai sani ba sai shi_. To amma su waye Rauhanan da wasu Malamai ko Shehunai da sauran wasu mutane suke ikirarin suna aiki da su? Malaman da suka kawo maganar Rauhaniy a littattafan _dibbu طب_ sun yi sa6ani akan asalin Rauhaniy da kuma menene shi.  Maganganu mafiya shahara d...