YADDA AKE HAƊA SABUNIƊ ƊAHARA. SABULUN KAMA RUWA NA MATA WANDA YA KE MAGANIN CUTUTTUKA. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
YADA AKE HAƊA SABUWNIƊ ƊAHARA.
Sabulun Kama Ruwa na Mata, Wanda Ke Magance Cututtuka Da kuma Gyaran Jikin Mace.
Abubuwan da ake Haɗawa
1- Sabulun Zaitun.
2- Sabulun Habbatus sauda.
3- Man Tafarnuwa.
4- Farin Almiski.
5- Ganyen Magarya.
6- Garin Bagaruwa.
7- Gasaya.
8- Ma'ul Khal.
Yadda ake yi.
A goga sabulun Zaitun da sabulun Habbatus sauda ko a daka su, su yi laushi. Sai a gyara ganyen magarya, atsince ƙayoyin da ke ciki a zubar, a haɗa ganyen magaryar da Gasaya a daka su, su yi laushi a zuba a kan garin sabulun a hautsina. Sai a tankaɗe garin Bagaruwa ya yi laushi, shi ma a zuba a kai, a hautsina. Sai a zuba man Tafarnuwa, shi a hautsina, a zuba farin Almiski shi ma a hautsina. Daga nan sai a zuba Ma'ul khal a kwaɓa sablun da shi.
Idan an tashi sai a cura sabulun ƙanana sosai, gwargwadon yadda duk sanda mace za ta yi amfani da shi za taɗauki guda ɗaya.
Sai a dinga amfani da ruwan ɗimi wajen kama ruwa da sabulun.
Amfanin Sabulun.
1- Tsaftace gaba.
Sabulun Zaitun da Ganyen Magarya da ke cikin haɗin na taimakawa wajen fitar da datti da tsaftace gaba.
2- Magance cututtuka.
Habbatus saudaa da Man Tafarnuwa da Ma'ul Khal da aka zuba suna kashe ƙwayoyin cuta da za a iya samu a cikin gaba.
3- Matsewa.
Gasaya da Bagaruwa da aka yi amfani da su na sakawa mace ta ƙara matsewa bayan haihuwa ko bayan buɗewa.
4- Saka ƙamshi.
Farin Miski na saka kamshi ga mace idan ta yi amfani da shi a gaba.
5- Maganin ƙaiƙayi da ƙuraje.
Habbatus sauda da Ma'ul khal da aka saka aciki za su taimaka wajen magance ƙaiƙayi da kashe ƙurajen gaba.
6- Ƙara sha'awa.
Farin miski da ƙamshi da ke ciki sabulun Habba da sabulun Zaitun za su taimaka wajen sa wa mace sha'awa bayan ta yi amfani da sabulun.
7- Santsi.
Matan da ke jin zafi lokacin saduwa za su dena saboda Man Zaitun na saka santsi da magance zafi ko raɗaɗi.
8- Magance wari.
Matan da ke da laurar fitar wari daga gabansu sabulun zai taimaka musu saboda ganyen magarya da ke ciki da Almiski.
Da dai sauran amfani da yawa.
Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya. 08162600700, 08134434846.
Comments
Post a Comment