AMFANIN NONON RAƘUMI KASHI NA BIYU. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
AMFANIN NONON RAƘUMI
(Kashi na biyu)
(8)CIWON SUGA.
Mai fama da larurar ciwon suga sai a samo: -
a) Nonon Raƙumi kofi daya.
b) Tirmis Baladi, cikin ƙaramin cokali
c) Garin Hulba, karamin cokali
d) Hubuwbul liƙah ƙaramin cokali
e)Markadadden bitter lemon ƙaramin cokali.
Sai a kaɗa su a cikin nonon, sai a sha kofi daya da safe
kofi daya da yamma tun kafin a ci abinci da awa daya,
ma'ana idan an sha maganin sai an samu awa đaya a tsakani sannan za a ci wani abu.
(9) CIWON CANCER
Wanda yake da wani ciwo da ya shafi cancer to
sai ya yi kokarin jarraba wannan maganin:
Zai rika shan kofi daya na nonon rakumi da safe da yamma amma tun kafin ya ci wani abu da awa daya. Ma'ana, ba zai ci wani abu ba zai sha maganin. Idan kuma ya sha maganin to sai ya
Samu awa daya a tsakani, sannan zai ci wani abu. Za
a yi haka a jere ba fashi tsawon kwana arba'in da
biyar. Sannan duk sanda ya sha wannan nonon to zai
sha shayin lipton ba madara cikin babban kofi tare da rabin kofi na fitsarin rakumi sai ya gauraya ya rika
sha tsawon adadin kwanakin.
Sannan shi kansa fitsarin rakumin idan an
tafasa shi da ruwa ana yin shayi lipton ba madara
ana sha, to magani ne sadidan
(10) CIWON SANYI
Idan mutum yana fama da ciwon sanyi, to sai ya
yi kokarin hada wadannan mahadđan, insha Allahu
zai fitsarar da sanyin da yake takura masa a jikinsa.
a)Nonon Raƙumi kofi daya
b) Kanunfari karamin cokali
c) Irƙu Dahab, ƙaramin cokali.
To sai ya hada ya sha kofi daya da safe, tun
kafin ya ci wani abu. Sannan kofi daya da yamma,
kofi daya da daddare. sharaɗi shi ne, duk sanda aka sha ba
za a ci komai ba sai an samu awa daya da rabi (1/2
hrs) a tsakani sannan za a ci wani abu.
(11) FITAR RUWA MAI WARI A GABAN MACE
Sanyi na iya sanya mace ta rika fitar da wani
ruwa mai wari, to maganin
wannan matsala shi ne, sai ta samu fitsarin rakumi
mai dama sai ta tafasa shi, sai ta rika shiga cikin
ruwan tana zama a ciki zuwa rabin awa, sannan ta fito. Za ta rika yin haka sau daya a rana, tsawo satin daya.
(12) RASHIN FITAR JININ HAILA
Sai ta samu madarar nonon rakumi ta sha kofi
daya da safe kofi daya da yamma, to in sha Allahu
za ta samu saukin lamarin.
(13) MAGANIN ƘURAJEN PIMPUS
Duk wanda kurajen pimpus suka dame shi suka
6ata masa fuska da fata, to sai ya samu madarar
nonon rakumi ya riƙa shafawa a kai, sannan kuma
yana shan kofi daya da safe da yamma, tsawon sati
biyu. To insha Allahu fatarsa za ta yi kyau, duk wasu
bakaken kuraje masu fesowa a jiki za su bace su
warke, fata za ta yi kyau da haske.
(14) ƘAIƘAYIN FATA
Duk wanda yake fama da soshe-soshen fata, da
karce-karcen fata, to, sai ya yi kokarin hada
wadannan mahadan:
a)Nonon Raƙumi
b)Hububul liƙahu
c) Fitsarin Rakumi
Da farko kullum zai sha nonon rakumi kofi uku
tare da Hububul Lika'hu karamin cokali a rana daya, safe da yamma da daddare, to amma tun kafin a ci
wani abu ake sha. In ma an sha sai an samu rabin
awa a tsakanı, sannan za a ci wani abu.
To, bayan ya sha wannan hadin, sai ya samu
fitsarin rakumi tare da man zaitun ya hada waje daya
ya rika shafawa a jikinsa sau uku a rana.
(15) ZAFIN FITSARI
Wanda yake fama da ciwon fitsari wato yana
fitsari da kyar, wani lokaci yana jin kamar ana kona
gabansa, to sai ya yi amfani da fujul wato ya
tafasa shi a cikin madarar Nono Raƙumi yana ci da safe tun kafin ya ci wani abu.
Abu na biyu mutum zai iya amfani da wadannan
mahaɗan:
a)Nonon rakumi kofi daya
b)Shammar karamin cokali
c) Halful Barri, ƙaramin cokali
Da farko idan an samu kofi daya na nonon rakumi to sai a zuba karamin cokali na garin Shammar sai a shanye shi sai kuma karamin cokali na garin
Halful Barri shi kuma tafasa shi za a yi a ruwa a rika
sha. Za a rika yin haka sau uku a rana amma sai an
ci abinci za a rika sha.
kafin ya ci wani abu.
(16) FITSARIN JINI
Mahadan su ne:-
a) Nonon Raƙumi
b) Kanin fari karamin cokali
c) Irƙu Dahabu rabin karamin cokali
Sai a zuba su a cikin nono a juya a sha safe da
yamma da daddare tun kafin a ci wani abu, idan
kuma an sha maganin to kar a ci wani abu a lokacin
har sai an samu rabin awa ½hr.
(17) CIWON SHAWARA
Mai ciwon shawara sai ya lazimci shan ruwa
kofi daya da safe tun kafin ya ci wani abu, sannan
kuma sai ya sha Nonon Raƙumi kofi daya tare da cin
kayan marmari kamar su ayaba gwanda, mangwaro
tufa, da dai sauransu
(18)DOMIN SAMUN ƘWARIN ƘASHI
Sai a samu wadannan mahadan:
a)Nonon rakumi
b)Fitsarin rakumi
c)Man Kafur
d)Man Na'a-na'a.
Da farko duk sanda ake cin abinci safe da rana
da na dare, to sai a sha kofi daya na nonon rakumi
sannan kuma sai a samu fitsarin rakumi sai a zuba man kafur da man Na'a-na'a, sai a juya shi sosai a riƙa shafe gaba dayan jiki da shi. Za a yi haka sau uku a yini.
(19) RAUNIN JI NA KUNNE
Mai fama da raunin ji na kunne, to sai ya yi amfani da auduga mai kyau sai ya jika ta da fitsarin rakumi, sai ya sa audugar a kunnuwansa tun daga yamma har zuwa wayewar gari, sai ya cire. To insha Allahu zai ji yadda kunnensa zai kasance dangane da ji sosai.
(20) MAGANIN DASKAREWAR JINI A JIKIN MUTUM
Mai fama da matsalar daskarewar jini, sai a samu
a)Nonon Raƙumi kofi ɗaya
b)Garin Habbur Rashad karamin cokali
c) Bizru Kattan, wanda aka daka shi, karamin cokali.
d) Garin citta mai laushi, karamin cokali
e)Hubbu Likahu karamin cokali.
Da farko idan aka samu nonon, to sai a zuba
wadannan mahadan a ciki, sai a sha kofi đaya da
safe tun kafin a ci wani abu, sannan bayan an sha za
a samu kamar rabin awa, sannan za a iya cin wani abu. Haka ma da yamma za a sha bayan an sha a sami rabin awa sannan a ci wani abu.
Daga shafin Bashir Halilu.
Lambar waya 08162600700.
Comments
Post a Comment