SHIN AN YI WA MANZON ALLAH ﷺ SIHIRI? KUMA SHIN SIHIRIN YA KAMA SHI? Daga shafin Dr. Bashir Halilu. Lambar waya 08134434846.
Wannan tambaya ce da wasu suke yawan yi: "Shin da gaske an yi wa Manzon Allah ﷺ sihiri? Idan an yi masa, ta yaya ya kasance? Amsa ita ce: Eh, an yi wa Manzon Allah ﷺ sihiri, kuma wannan ya tabbata a cikin ingantattun hadisai. Amma sihirin bai shafi isar da saƙon Allah da wahayi ba. Wato sihirin ya saka Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama rashin lafiyar jiki ne amma ta ɓangaren addini da isar da saƙon Allah komai dede ya ke yi. An karɓo daga Nana A’isha رضي الله عنها ta ce: «سَحَرَ رَسُولَ اللَّهِ ﷺ رَجُلٌ مِنْ بَنِي زُرَيْقٍ يُقَالُ لَهُ لَبِيدُ بْنُ الْأَعْصَمِ» Ma’ana: “Wani mutum daga ƙabilar Banu Zuraiq, mai suna Labīd ɗan Al-A‘ṣam, ya yi wa Manzon Allah ﷺ sihiri.” Hadisin ya bayyana cewa tasirin sihirin ya kai ga Annabi ﷺ yana tsammanin ya aikata wani abu alhali bai aikata shi ba. Daga baya Allah Ya sanar da shi abin da ya faru, kuma Ya ...