ƘISSAR SHAIƊAN DA MASU BAUTAR BISHIYA

Da akwai wasu mutane da suke bautawa bishiya a matsayin Ubangijinsu.
   Ana nan sai labarinsu ya je kunnen wani mai-bautar-Allah, sai abin ya ɓata masa rai, don haka sai ya ɗauki gatari ya tafi don ya sare wannan bishiyar. Yana cikin tafiya sai Shaiɗan ya tare shi a hanya, ya ce masa "Ya kai bawan Allah, ina za ka da gatari haka?". Sai mutumin ya ce ma sa "Ai wasu mutane ne suke bautawa bishiya, shi ne zan je na sare ta".  Sai Shaiɗan ya ce masa "Ka haƙura kawai ka koma gida, ai Allah Ya san suna bautar bishiyar amma Ya ƙyale su. Da ba ya so su yi ai da ya aiko Annabi don ya hana su". 

     Sai mutumin nan ya ce "Ni dai sai na je". Sai suka kama kokawa da Shaiɗan, mutumin nan ya ɗaga Shaiɗan ya doka shi da ƙasa.

   Da Shaiɗan ya ga haka sai ya sake cewa mutumin nan "Ka ga kai talaka ne, ba ka da komai. Don haka kullum zan dinga baka dinare guda biyu amma ka kyale su su cigaba da bautawa bishiyarsu"

   Sai mutumin nan ya ce "To na yarda" Sai ya koma gida.

      Da gari ya waye sai Shaiɗan ya kawo masa dinare biyu ya ba shi, mutumin ya kar6e ya kashe. Kullum sai Shaiɗan ya kawo masa kuɗi, shi kuma ya kar6a.

     Ana nan rannan sai gari ya waye Shaiɗan bai kawo kuɗi ba, rana ta biyu ma Shaiɗan bai kawo ba har kwana uku.

    Da mutumin nan ya ga haka sai yay fushi, ya ɗauki gatarinsa, ya koma zai sare bishiyar nan.

   Sai Shaiɗan ya sake tare shi a hanya, ya hana shi, mutumin nan ya ƙi haƙura. 

    Sai suka kama kokawa, sai Shaiɗan ya ɗaga mutumin nan ya damfara shi da ƙasa.

Sai mamaki ya kama mutumin nan, ya cewa Shaiɗan "Ya kai Shaiɗan!, ya akai da farko mu kay faɗa na samu nasara a kanka amma yanzu kuma kai ka samu nasara a kaina?". Sai Shaiɗan ya ce masa "Abinda yasa ka samu nasara a kaina da farko saboda ka fito aikin Allah ne, shi yasa Allah ya ba ka karfi ka kayar dani. Yanzu kuma ka fito ne don son zuciyarka, don van ba ka cin hanci ba, ba don Allah ka fito ba, shi ya sa na samu nasara a kanka". 

(Littafin Al-Iblis_الإبليس).

 Daga shafin Bashir Halilu.

Comments

Popular Posts