AMFANIN SASSAƘEN BISHIYAR GAMJI. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
AMFANIN SASSAKEN BISHIYAR GAMJI.
Ana tafasa sassaken Gamji ko a jika shi, shi kadai, a dinga sha don magance cututtuka da kuma kyautata lafiyar jiki.
Ana kuma kiran bishiyar Gamji da suna Danko.
A turance kuma ana kiransa 'Flake rubber tree'.
Fa'idodinsa wajen kyautata lafiya
1- Shan ruwan sassaken Gamji, wanda aka jika ko aka dafa yana karawa mutum yanayin jiki mai kyau. Wato ka ga jikin mutum ya yi sumul-sumul, ya kara kyan gani.
2- Gamji na kara yawan ruwan nono, ga mata, masu shayarwa.
3- Yana maganin ciwon ciki.
4- Gamji babban sinadari ne mai matukar kara yawan jini ajikin mutum.
5- Yana maganin gudawa ga yara da manya.
6- Yana magance matsalolin cikin ciki.
7- Yana magance matsalar shafar Aljanu.
8- Shan ruwan sassaƙen Gamji yana sa jin yunwa, ma'ana yana sa mutum cib abinci sosai.
Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700.
Comments
Post a Comment