AMFANIN KANUMFARI WAJEN KYAUTATA LAFIYA. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846

AMFANIN KANUMFARI WAJEN KARA LAFIYA. 
Daga shafin Magunguna a Musulunci. 
https://www.facebook.com/groups/842715785785303/
Lambar waya 08162600700.

1. CIWONKAI
    Kanumfari yana maganin ciwon kai idan aka shafa mansa a goshi, yana taimakawa
wajen ciwon kai wanda ke faruwa
sanadiyar mura. Idan kuma ciwon kan ba na mura bane, za'a iya samun Kanumfari guda biyar a saka a cikin ruwa kofi guda, a saka a wuta su tafasa sosai sai a saka Sugar kamar Rabin cokali a ciki idan ya dan huce sai a sha ayi haka sau 2 a yini
In shaa Allahu kan zai daina ciwo koda kuwa baya jin Magani ne.

2. CIWON HAKORI.
Yana maganin ciwon hakori. Zaka
iya amfani da man-kanimfari (clove oil)
ga hakori mai-ciwo ko kuma kanimfarin
(dakakke) , a jikashi kadan da ruwa a lika wajen hakori mai-ciwo. Idan man( clove oil) kake amfani dashi sai asamu auduga a zuba man kadan alika wajen hakori mai-ciwo (ka danne da
hakora).

3.WARIN BAKI.
Za’a iya amfani dashi amatsayin
abun wanke baki. Yana maganin warin
baki (a tafashi a yawaita wanke baki
dashi sau 3 a rana).

4.MAGANIN AMAI
(A), Domin Tsayawar amai ga Mata masu
ciki, a daka kanunfari biyu a sa babban
cokali daya na zuma a sha yana maganin
Amai ga macce mai ciki.
( B)Don magance amai baga mai juna biyu ba kuwa, a saka kanumfari 4 a cikin ruwa kofi daya a tafasa idan ya tafasa a saka sugar cokali daya a sha.

5.TYPHOID
A samu ruwa littr biyu sai a saka kanumfari kamar guda 5 a cikin ruwa a tafasa ruwan kada a sauke sai ruwan sun koma sauran littr daya sai a sauke idan ruwan ya huce sai a riqa shan Wannan yana Maganin typhoid.

6. Ciwon Kunne;
A hada Man kanun fari da Man Ridi a diga a kunne mai ciwo duk lokacin da za'a kwanta wannan yana maganin ciwon
kunne.

7.MAGANIN MURA
Ga masu yin mura a tafasashi da citta/jinja(ginger) a sha shayi.
8. MAGANCE MAKERO/KYANDA
Ana goga Man kanumfari a wurin da matsalar take wannan yana maganin Makero.

9. GIRMAN MAZAKUTA
Asamu nikakken kanumfari ko adakasa
sai ajikasa da mansa ahada da man zaitun, sai ajika "gaba" dashi,idan za'a kwanta, da rana kuwa duk bayan anyi wanka sai ashafa, wannan yana sa girman Azzakari.

10. KARFIN MAZAKUTA
A samu Man kanumfari duk za'a yi saduwar aure awa daya kafin a fara a shafe gaba da shi.

11. KURAJEN HARSHE
Don Magance Kurajen Harshe, daka Kanumfari a saka a harshen a barshi tsawon wani lokaci, ko kuma idan za'a kwanta a saka in shaa Allahu kafin safe zasuyi dama.

Daga cibiyar ALBISHIR ISALAMIC MEDICINE

https://www.facebook.com/groups/842715785785303/
Lambar waya 08162600700.

1. CIWON SUKARI (DIABETES)
A wani bincike da aka gudanar a shekarar 2006, an gano cewa kanunfari na taimakawa wajen rage yawan
sikarin da ke cikin jini, a don haka yana
matukar taimakawa masu ciwon sikari. Yadda ake amfani da shi Za a iyabzuba kimanin gram 10 na dakakken kanunfari a cikin ruwan
dumi a sha shi da safe kafin a ci komai, ko kuma a barbada shi a cikin abinci.

2.MAGANCE MATSALOLI DA CIWON BAKI
Kanunfari da man shi na da tasiri akan kowane irin cuta ta baki, kama daga ciwukan hakori zuwa warin baki ko kumburin dasashi da sauran su.
Dalili kuwa shi ne ya na dauke da sinadaran da ke kashe kwayoyin cuta da kuma rage radadin ciwo.
Yadda ake amfani da shi Ga mai ciwon hakori, za a iya shafa man kanunfari ko kuma a tauna kanunfarin kan shi domin samun sauki cikin gaggawa.
Idan kuma mutum yana fama da warin baki ne, to zai tafasa kanunfarin a cikin ruwa, idan ya huce, za a dinga amfani da shi wajen kurkure baki bayan cin kowane abinci.

3.MAGANCE CIWON GABOBI
Kanunfari na dauke da sinadaran da ke rage radadi da kuma kumburi, wannan ya sa ya ke da matukar tasiri ga masu ciwon gabobi Yadda ake amfani da shi Za a nade garin kanunfarin a cikin tsumma
mai tsafta a dan dumama shi a wuta, sannan a dora shi a gurin da yake ciwon, ko kuma ana zuba man kanunfarin kadan a cikin ruwan
wanka.

4. MAGANCE CIWON MAQOGARO
Kasancewar shi dauke da sinadaren dake kashe kwayoyin cuta da rage radadi, kanunfari na da matukar tasiri
akan ciwon makogwaro.
Yadda ake amfani da shi Za zuba kanunfari guda gudan shi a zuma, a barshi na kamar tsahon awanni 8. Bayan haka sai a sha zumar da kadan da kadan ta yadda zumar zata na rufe cikin makogwaron da ke ciwo.

5. MATSALOLIN FATA
Kanunfari na tasiri akan matsalolin fata kamar su kuraje, dabbare dabbare, kumburi da sauransu. Yadda ake amfani dashi Za a iya hada garin kanunfari da Zuma da lemon tsami ana shafawa a gurin da yake da matsalar.

6.DOMIN KARIN NI'IMA
kamar yanda mata ke ajiye Zuma agida haka yanzu mata basa rabuwa da kanunfari domin duk wani hadin daka na musamman ko hadin ruwan jaraba ko wani tsumi idan kuka bincika.zakuga akwai sa hannun kanunfari don haka kema ki ajiye shi don burge mijinki duk lokacinda zaki dafa shayi kada kimanta dashi domin idan ya hadu da lifton yana aiki ajikin mace wajen karin ni ima kuma yanada kyau ajinki ya zama akwai kunfari aciki

7.RAGE KIBA (LOSE WEIGHT)
Ana Amfani da kanimfari wajen rage tumbi ki jika shi aruwa idan ya yini ajike sai kishanye ruwan ki kara wani zaki ga cikin ki yasaki kinyi bayan gida wannan shine alamar yayi miki aiki

8.INFECTION
(A).Ana Amfani da Kanimfari wajen maganin infection idan kika saka ruwa tafasashe a copy flast sai ki zuba shi aciki da ganyen magarya kirufe sai yayi kamar sa'a daya (1 hour) zaki yini
kina yin tsarki dashi har zuwa dare
(B)Zaki iya daka garin kanimfari kihadashi da totuwar raken dakika sha yabushe sai ki sami farin muski (miskul dahra) ki cakuda shi sosai da garin da tutowar raken da kuma muskin idan yabushe sai ki ringa turaren tsugunawa dashi wannan kada ki barshi. 

Daga cibiyar ALBISHIR ISLAMIC MEDICINE. 
https://www.facebook.com/groups/842715785785303/

Lambar waya 08162600700.

Comments

Popular Posts