AMFANIN ALBASA DA TAFARNUWA DA CITTA WAJEN ƘARA LAFIYA. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
AMFANIN ALBASA DA TAFARNUWA DA CITTA WAJEN KARA LAFIYA.
Daga Cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci.
Shiga shafinmu na youtube domin samun bidiyo na magunguna acikin wannan shudin rubutun
https://youtube.com/channel/UCw1NWWsxJJbQkXcqHA127GA
Labar waya 08162600700, 08134434846.
AMFANIN ALBASA DA TAFARNUWA DA CITTA WAJEN KARA LAFIYA.
Daga Cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci.
Shiga shafinmu na youtube domin samun bidiyo na magunguna acikin wannan shudin rubutun
https://youtube.com/channel/UCw1NWWsxJJbQkXcqHA127GA
Labar waya 08162600700.
AMFANIN ALBASA
Hakika albasa na da tsohon tarihi duba da yadda al'umma ke amfani da ita a harkokin abincinsu da kuma magani. Masana sun yi ittifakin cewa albasa na da wasu muhimmman sanadarai da ke taimakawa wajen gina jikin dan-adam, baya ga haka sinadaran da albasa ke kunshe da su na da tasiri kan wasu cututtukan jiki.
Shekaru da yawa da su ka shude, al'ummomin Duniya daban-daban ke amfani da albasa don magance cututtukan da ke damun su, kamar ciwon sanyin kashi, mura, ciwon makogoro da gabobi da sauran su.
1. Maganin Tari, Mura Ko Ciwon Makogoro.
Daga cikin amfanin albasa ga dan-adam akwai maganin sanyi, mura ko ciwon makogoro. Duk wanda ke fama da daya ko duk ciwon da muka zana a sama, musamman wanda ke fama da tari ko mura mai tsanani, ya nemi man Albasa cikin babban cokali 9, da zuma babban cokali 9, sai ya zuba man albasar cikin zumar ya gauraya sosai, daga nan sai ya samu mazubinsa mai tsafta kuma mai murfi ya adana ya arika shan cokali uku a kullum, wato safe, rana da dare.
2. Maganin Zafin Fitsari.
Ana amfani da albasa don magance matsalar fitar fitsari da zafi. Ga mutumin da ke shan wahala wajen fitar fitsari, ya nemi man albasa ya hada da zuma mai kyau da lemon tsami ya gauraya, ya tabbatar sun gaurayu sosai, sai ya dinga sha sau biyu a rana, ma'ana da safe da yamma, sannan kuma ya rika shafa man albasa ajikin mararsa.
3. Maganin Sanyin Kashi
Albasa na maganin sanyin kashi. Duk mai fama da wannan matsala ta sanyin kashi , sai ya samu albasa ya dafa Albasa ya dafa ta, ya zuba man zaitun a rika dumama wajen da ya ke jin ciwon, sannan da dare kafin ya kwanta barci sai ya shafe wajen ciwon da wannan hadin, sannan kuma ya rinka sha da safe, haka za ayi har tsawon kwana bakwai. In sha Allahu za'a dace.
4. Maganin Maruru Ko Kuraje.
Hakanan, daga amfanin albasa ga lafiyarmu, har da maganin kuraje ko maruru. Yadda za a yi shine, a samu albasa a kirba ta, sai a hada da man zaitun a dafa ake wanke marurun ko kurajen, bayan an kammala wanke wa, sai a shafa man zaitun a gurin.
5. Maganin Zubar Gashi.
Ina matan da ke fama da zubar gashi?, za ku iya yin amfani da albasa domin magance wannan matsala. Duk matar da ke fama da zubewar gashi, ta samu ruwan albasa, ta hada da man Simsim, da kuma garin Baqadunas, ta dinga shafewa kanta da shi, ta tabbatar ta game kanta tun daga matsirar gashinta. Za ta yi haka a kullum kafin ta kwanta barci. Idan gari ya waye sai ta wanke da ruwan dumi. Haka za ta yi har tsawon mako guda. Da yardar Ubangiji za ta samu biyan bukata.
6. Maganin Lagwada.
Amfanin albasa ga lafiyar dan-adam ya hada da tasirinta wajen maganin kurajen lagwada, idan mutum na fama da wannan matsala, sai ya samu ruwan albasa ya hada shi da ruwan Kahl a saka a wajen a daure sai bayan kwana daya ko biyu sai a kwance idan bata cire ba sai a maimaita har sai ta cire. Allah Ya sa mu dace,amin.
7. Maganin Karfin Mazakuta.
Masana sun nuna cewa, daga cikin amfanin albasa ga lafiyarmu, akwai maganin karfin maza. Ga mai son ya amfana da wannan fa'ida ta albasa sai ya samu kofi daya na ruwan zuma mai kyau, marar hadi da rabin kofi na ruwan albasa, sai ya zuba cikin tukunya ya dora kan wuta idan ya fara tururi sai ya sauke sai a rinka shan babban cokali daya sau 3 a kullum.
8. Maganin Amosanin Ka.
Har-ila-yau daga cikin amfanin albasa ga lafiyar dan adam, har da maganin amosanin ka, duk matumin da ke fama da amosanin ka, sai ya samu ruwan albasa, ya hada da man Simsim, da kuma garin Baqadunas, ya dinga shafewa kansa da shi, ya tabbatar ya game kansa tun daga matsirar gashi. Zai yi haka a kullum kafin ya kwanta barci. Idan gari ya waye sai ya wanke da ruwan dumi. Haka zai yi har tsawon mako guda. Da yardar Ubangiji zai samu biyan bukata.
9. Maganin Daji (Cancer) Na Fata.
Ana yin amfani da albasa wajen maganin ciwon dajin fata. Idan mutum ya na fama da wannan matsala sai ya samu ruwan albasa, da garin hulba da karamin cokali na farar wuta. Zai hada ruwan albasar da garin hulba da kuma farar wutar waje guda ya gauraya su, sai ya ke shafawa a wajen ciwon safe da yamma tsawon mako biyu.
10. Albasa Na Taimaka Wa Ma Su Ciwon Sikila.
Daga cikin irin amfanin albasa ga lafiyar bil adama, akwai taimaka wa ma su fama da cutar sikila. Idan mutum na fama da wannan matsala ta sikila sai ya rika yanka albasa tare da ganyen Zogale yana ci. Insha Allahu, zai samu saukin ciwon Sikila din.
11. Albasa Na Inganta Lafiyar Jikin Dan Adam.
Bayanin masana ya tabbata kan yadda albasa ke inganta lafiyar jikin bil adam. Duk mutumin da ke fama da matsalar karancin jini, ya yawaita cin albasa. insha Allahu jininsa zai yawaita.
12. Albasa Na Taimaka Wa Mai Ciwon Siga.
Mai fama da ciwon siga zai iya amfani da albasa don samun sauki musamman a yanayin fitar fitsari da yawa cikin dare. Saboda haka duk mai fama da yawan fitar fitsari sakamakon ciwon Siga ya nemi albasa mai kyau ya rika yankawa kullum yana ci. Idan Allah Ya so, sigansa zai sauka, kuma zai dena yawan fita fitsarin.
13. Albasa Na Maganin Kwarkwata.
Amfanin albasa ga lafiyar dan adam, ya hada da maganin kwarkwata, duk matar da ke fama da kwarkwata, sai ta samu ruwan albasa, ta hada da man Simsim, da kuma garin Baqadunas, ta dinga shafewa kanta da shi, ta tabbatar ta game kanta tun daga matsirar gashi. Za ta yi haka a kullum kafin ta kwanta barci. Idan gari ya waye sai ta wanke da ruwan dumi. Haka za ta yi har tsawon mako guda. Da yardar Ubangiji za ta samu biyan bukata.
AMFANIN TAFARNUWA WAJEN KARA LAFIYA
Daga Cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci.
Shiga shafinmu na youtube domin samun bidiyo na magunguna acikin wannan shudin rubutun
https://youtube.com/channel/UCw1NWWsxJJbQkXcqHA127GA
Lambar waya 08162600700.
Tafarnuwa na kunshe da sinadaran, saponin, phosphorus, potassium, sulfur, da zinc ma su yawan gaske a cikinta sannan ta na kunshe da matsakaicin adadin sanadaran, selenium da bitamin A da C. Sai kuma kadan daga sinadaran, calcium, magnesium, sodium, Iron, manganese, da kuma B-complex Vitamins.
Wadannan sinadarai da mu ka ambata a sama, wadanda kuma tafarnuwa ke da su, na da matukar tasiri wajen inganta lafiyar jikin mutum da kuma samar da magani kan wasu cututtuka.
Wasu daga amfanin tafarnuwa su ne
1. Bunkasa Garkuwar Jiki.
A wani bincike da manazarta su ka gudanar kan kwayoyin halittar dan-adam (cells) dangane da amfanin tafarnuwa ga lafiya, sun gano cewa, tafarnuwa na inganta kwayoyin halittar jini, da ake kira "White blood cells" da turanci, ta hanyar kara adadin wani sanadari da ake kira 'glutathione' a turance. To su Kwayoyin halittar jinin da ake kira 'White blood cells' su ne ke samar wa jiki kariya daga cututtuka. A takaice, ka iya cewa, su ne garkuwar jikin dan-adam. Wannan ya sa tafarnuwa ke taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa garkuwar jikin dan-adam ta samu damar fatattakar duk wata cuta da ka iya kai wa jikin farmaki.
2. Maganin Mura
Daga cikin amfanin tafarnuwa ga lafiyarmu, akwai maganin mura. Binciken masana kiwon lafiya ya tabbatar da yadda ake amfani da tafarnuwa wajen samun saukin mura da dangoginta da kan shafi makogoro, kirji da hanci da sauran su. Wani nazari da aka gudanar kan wasu mutane 120, ya nuna cewa baya ga maganin mura da tafarnuwa ke yi, hakanan yawan amfani da ita na bai wa jiki riga-kafin kamuwa daga murar.
Ga duk mutumin dake fama da mura, kuma ya ke son amfani da tafarnuwa don samun sauki, sai ya ci salar tafarnuwa 2 zuwa 3 a rana, ko kuma ya hada shayin tafarnuwa. Abubuwan da zai hada shayin sun hada da tafarnuwar ita kanta, da kuma citta, da zuma. Zai sha wannan shayi sau biyu a rana, da safe da yamma kenan.
3. Rigakafin Kamuwa Da Cututtukan Zuciya.
Yin amfani da tafarnuwa a kullum, a cikin abinci ko kuma danyarta, na taimakawa wajen rage yawan adadin sanadarin' cholesterol' saboda ta na aiki irin na 'anti-oxidant' sakamakon sandarin 'Allicin' da ta ke kunshe da shi. Har ila yau, tana da amfani sosai wajen daidaita hawan jini da kuma daidaita yawan sigan dake cikin jini. Sakamakon haka ne ya sa masana kiwon lafiya su ka nuna tafarnuwa na inganta lafiyar zuciya da kuma ba ta rigakafin kamuwa da cututtukan da kan shafi zuciya.
4. Gyaran fata Da Kuma Gashi.
Daga cikin amfanin tafarnuwa ga lafiyar dan-adam, har da gyaran fata da kuma gashi. Bincike ya nuna cewa, tafarnuwa na da wasu sandarai da ke dakile yamushewar fata, sannan kuma wasu sanadaran na tafarnuwa na da amfani wajen hana zubewar gashi.
Kamar yadda masanan su ka bayyana abubuwan ban al'ajabi da albasa ke yi dangane da gyaran gashi, sun bayyana cewa, amfanin 'yar uwarta, tafarnuwa ya zarta na albasa. Mutum zai samu fa'idar tafarnuwa dangane da gyaran fata da gashi ta hanyar shafa dandakakkiyar tafarnuwar, ko kuma shafa man tafarnuwar a gindin gashi don hana zubewar gashi ko karyewarsa.
Hakanan, wannan hadin na kara yawan gashi da kuma hana shi karyewa. Ki samu man tafarnuwa, ki hada shi da man kwakwa da man zaitu ki rinka shafawa a kanki. Ana son ki tabbatar kin game kanki da wannan hadi ta hanyar murzawa yadda zai samu matsirar gashinki. Za ki ga abin mamaki.
Baya ga gyaran fata da tafarnuwa ke yi, hakanan, ta na bayar da kariya ga fatar wajen kamuwa daga wasu cututtukan fata.
5. Saukar Da Hawan Jini
'Angiotensin II', wani sanadari ne dake haddasa matsewar jijiyoyin jini, sakamakon haka sai ya haifar da hawan jini. To akwai wani sanadari dake cikin tafarnuwa mai suna 'Allicin' wanda ke hana aikin sandarin Angiotensin II, wanda hakan ke taimaka wa wajen rage hawan jini.
Baya ga haka akwai wasu sanadari dake cikin tafarnuwa mai suna 'polysulphi' da kwayoyin halittar jini mai launin ja(Red Blood Cells) ke rikidar da shi zuwa wani sanadari da ake kira 'hydrogen sulphide. Shi wannan sanadarin ne ke sassauta matsewar jijiyoyin jini, sakamakon haka sai ya taimaka wajen saukar hawan jini.
6. Taimakawa Matsalolin Numfashi.
Kamar yadda mu ka ambata a sama cewa yin amfani da tafarnuwa yau da kullum na rage wa tare da maganin mura da sanyi. Baya ga maganin kaikayin makogwaro.
Kari kan haka, tafarnuwa na iya maganin cututtukan da ke da alaka da numfashi. An tabbatar da cewa, tafarnuwa na taimakawa mutanen da ke shan wahalar numfashi, kamar ma su cutar Asma ko kuma murar da ta yi tsanani har ta haddasa shakewar hanyar numfashi da sauran su.
7. Ciwon Hakori.
Sanya dandakakkiyar tafarnuwa a kan hakorin da ke ciwo zai iya taimakawa wajen samun saukin ciwon hakori, sakamakon aikin 'antibacterial da 'analgesic' da tafarnuwar kan yi. Amma ya na kyau ka san cewa, tafarnuwa kan haifar da radadi kan dasashi.
8. Riga-kafin Ciwon Daji
Har ila yau dai, daga cikin amfani tafarnuwa ga lafiyarmu, akwai riga-kafin kamuwa daga cutar daji. Masanan sun ce, amfani da tafarnuwa yau da kullum na rage hadarin kamuwa da ciwon daji. Tafarnuwa na taka wannan muhimmiyar rawa ne, sakamakon sandaran 'allyl sulphides' da tafarnuwa ke da su. Su wadannan sanadarai ne ke aikin samar wa jiki riga-kafin kamuwa daga cutar daji.
9. Ciwon Ciki Bayan Haihuwa.
Wasu mata kan fuskanci matsalar ciwon Ciki Ko kullewar mara bayan sun haihu, kuma wannan matsala kan ci mu su tuwo a kwarya, har su galabaita. To ga matar dake fama da wannan matsala, sai ta yi amfani da tafarnuwa. Ta samu man tafarnuwa babban cokaki daya, sai ta zuba cikin ruwan zafi kofi daya. Za ta sha sau uku a kowacce rana har tsawon kwanaki uku.
10. Ciwon Mara Lokacin Jinin Al'ada
Tafarnuwa na da amfani ga mata, musamman ma matan da ke fama da ciwon mara a duk lokacin da jinin al'ada ya zo mu su. Ga macen da ke fama da ciwon mara ko ciwon ciki lokacin al’ada, ta samu man tafarnuwa ludayi guda, da zumarta mai kyau wacce ba ta da algus ludayi biyu, sai ta hade su waje guda a mazubinta mai tsafta ta adana shi. Daga nan sai ta ke shan cokali biyu da safe, cokali biyu da yamma.
Hakazalika, wacce jinin al'adarta ya ke ma ta wasa, ita ma wannan hadin za ta yi, kuma yadda mai waccar matsalar ta sha ita ma haka za ta sha.
11. Tafarnuwa Na Taimaka Wa A Samu Isashen Barci
Ga mutanen da ke fama da rashin samun barci, sai su yi amfani da tafarnuwa don su samu isasshen barci. Ga yadda za su yi, tun farko su samu zumarsu mai kyau da kuma tafarnuwa, amma sai su daka tafarnuwar don su samu garinta, sai su zuba garin tafarnuwar rabin ludayi cikin zumar su gauraya yadda za su hadu sosai, suke shan babban cokali daya sau uku a kullum. Sannan kuma su samu man tafarnuwa su ke shafewa jikinsu.
AMFANIN CITTA WAJEN KYAUTATA LAFIYA

Citta, ana yin amfani da ita wajen hada magungunan ciwon jiki da na inganta lafiya a dukkan fadin duniya, daruruwan shekaru da su ka wuce. Misali al'ummar kasar Misra na amfani da Citta don maganin ciwon gabobi, zafin jiki, hana kumburi, da kuma hana amai da tashin zuciya.
Citta na kunshe da wasu muhimman sanadarai na inganta lafiyar Dan'Adam, da kuma ba shi kariya da kamuwa daga wasu cututtuka.
Ga wasu daga cikin amfanin Citta.
1. Maganin Ciwon Jiki.
Mun bayyana a sama cewa, shekaru aru-aru da su ka shuda, al'ummomi daban-daban na duniya ke amfani da citta don maganin ciwon gabobi, baya ga ciwon gabobi, har ila yau, su na amfani da citta don maganin ciwon jiki, kuma haka al'amarin ya ke har a gobe. Saboda citta na da wasu sanadarai da ke hana ciwon jiki sakamakon aikin karfi ko na gajiya da aka gudanar.
Ɗaya daga cikin binciken da aka wallafa a mujallar 'Journal of Pain' ya gano cewa, mutanen da ke wasannin motsa jiki na yin amfani da hadin da aka sarrafa daga citta don maganin ciwon jiki bayan sun kammala wasannin motsa jiki.
Hakanan, mutanen da ke son su wayi gari cikin kuzari da walwala, ba sa kwantawa barci ba tare da shan shayin da aka hada da citta ba. Yin hakan kan sa su wayi gari cikin kuzari da walwala.
2. Maganin Rudewar Ciki
Idan ka tattauna da wanda ya lizamci shan shayin da aka hada da citta, zai ba ka labarin yadda cikinsa ke kasancewa cikin koshin lafiya. Kuma kai kanka da za ka ke yin amfani da citta da za ka gane amfanin cittar wajen samar da lafiyar ciki, saboda ta na maganin rudewar ciki, tashin zuciya, kwarnafi da sauran su.
Wani mai wallafa rahotanni kan kiwon lafiya mai suna, Marissa Miller, ya bayyana amfanin citta ga lafiyar dan-adam da cewa, abin sha ne mai kyau da ya kamata mutane su ke sha, musamman bayan cin abinci mai nauyi.
"Shan Kofi daya na shayin citta, zai iya taimakawa mutum ya samu lafiyar ciki sauri, musamman a yanayin da ya ci abinci mai nauyi, don kuwa za ta taimaka ma sa wajen samun sassaucin cikinsa," inji Kamar Miller.
3. Maganin Ciwon Mara Lokacin Jinin Al'ada
Saboda yadda masana ke kiran citta da "anti-inflammatory" ya sanya ta ke taimakawa wajen maganin ciwon marar mata lokacin da su ke jinin al'ada. Manazarta sun ce, dangane da maganin ciwon mara lokacin jinin al'ada citta na aiki kwatankwacin maganin nan na zamani mai suna 'Ibuprofen'. Wannan sakamakon wani bincike da aka gudanar ne a shekara ta 2009, sannan aka buga a wata mujalla mai suna "Journal of Alternative and Complementary Medicine".
Wannan wani labari ne mai dadi ga dukan matan da ke fama da ciwon mara a lokacin da suke jinin al'ada. Da zarar kin ji ciwon ciki idan al'adarki ta zo, shan kofi daya na shayin citta kawai zai iya taimaka miki ki samu sauki, kuma ki ci gaba da harkokinki.
Karanta: Maganin Ciwon Mara Lokacin Jinin Al'ada.
4. Maganin Sanyi da Mura
Hakika citta ta yi fice wajen maganin matsalolin sanyi da mura saboda wasu sanadarai da cittar ke kunshe da su, sakamakon haka ne ya sa cittar ke iya taimaka wa wajen yaki da sanyi ko kamuwa da cututtukan makogoro.
Domin maganin matsalar mura, "Ka zuba babban cokali biyu na tacaccen ruwan danyar citta, cikin ruwan zafi kofi daya, da lemon tsami guda daya, sannan ka zuba cokali daya na zuma," in ji Miller. ka sha wannan hadin citta safe da yamma. "Ko kuma, ka zuba citta babban cokali daya cikin romon da aka dafa kaza don maganin mura, ko kuma riga-kafin kamuwa da sanyi."
5. Inganta Lafiyar Kwakwalwa
Wani bincike da manazarta su ka gudanar a shekara ta 2011, kuma aka wallafa a mujallar "Evidence Based Complementary and Alternative Medicine" ya nuna cewa citta na da wasu muhimman sanadarai da ke taimakawa kwakwalwa ta yi aikinta yadda ya kamata.
Baya ga taimakawa kwakwalwa yin aikinta yadda ya dace, haka kuma cittar ke taimawa wajen hana mantuwa, sakamakon inganta lafiyar kwakwalwarmu. A takaice dai ka iya cewa, citta na kara kaifin basira ga dan-adam.
Karanta: Illolin Tsarki Da Sabulu Ga Mata.
6. Rage hadarin Kamuwa Da Cutar Daji
Akwai wasu bincike da masana da yawa su ka gudanar, kuma sun nuna cewa, citta na da wasu sanadarai da ke bai wa jiki kariya wajen kamuwa da ciwon daji, kuma binciken ya nuna citta na kunshe da wadannan sandarai ma su yawan gaske.
Wani nazari da masana kiwon lafiya su ka gudanar a shekara ta 2012, kuma aka buga a jaridar "British Journal of Nutrition", ya gano cewa, citta na da tasiri kwarai wajen hana kamuwa da ciwon daji. Kodayake, binciken na matakin farko ne, a lokacin da jaridar ta wallafa sakamakon binciken, amma ana fatan samun ci gaba a wannan fannin.
7. Saurin Narkar Da Abinci
Wani lokacin mu kan samu kanmu cikin tsanani idan mu ka ci abinci, amma ya ki narkewa akan kari, Yanzu an gano za a iya amfani da citta don shawo kan wannan matsalar. Kofi daya na shayin citta zai iya taimakawa wajen narkewar abinci cikin sauri, kamar yadda Dokta Christy Brissette, wani likita a fanni abinci mai gina jiki ya bayyana.
8. Maganin Amai Da Tashin Zuciya
Wani bincike ya nuna cewa, citta na taimakawa wajen maganin amai da tashin zuciya, shin aman ko tashin zuciyar na larura ne da ke faruwa sakamakon wata rashin lafiya ko kuma amai ne ko tashin zuciya irin na mata ma su ciki ?. A kowanne yanayi citta na taimakawa.
Shan kofi daya na shayin citta, wanda aka hada da cokali daya na zuma na bayar da sakamako mai kyau, kamar yadda masanan su ka bayyana.
9. Ragewa Kwalastaral Maras Kyau
Wani manazarci mai suna, Brissette ya bayyana cewa, citta na iya taimakawa wajen rage yawan 'cholestero lLDL' marar kyau, wanda hakan kuma ke rage yawan hadarin kamuwa da cutukan zuciya. Wani binciken da aka gudanar kwanan nan ya tabbatar da sakamakon wannan binciken, inda ya nuna cewa, wani rukunin mutane da aka gudanar da binciken a kansu, sun kasance su na cin giram 3 na citta, kwatankwacin rabin karamin cokali, sau uku a rana sun sami raguwar 'cholesterol' a jikinsu fiye da rukunin da ba sa cin cittar.
10. Inganta Lafiyar Zuciya
Kamar yadda ya ke rubuce a sama cewa, bincike ya tabbatar da yadda yin amfani da citta ke rage yawan Kwalastaral marar kyau a jikin mutum, sannan, binciken ya nuna cewa, yawan kwalastaral a jiki ko akasin haka na da kyakkyawar dangantaka da lafiyar zuciyar dan-adam. Saboda haka tun da citta na iya rage yawan kwalastaral marar kyau a jikin mutum, ba shakka hakan na kara inganta lafiyar zuciya, ta yi aikinta yadda ya kamata, sannan ta samu kariya daga cututtukan da kan shafi zuciyar.
11. Bunkasa Garkuwar Jiki
Amfanin citta ga lafiyar dan adam ya hada da kara karfin garkuwar jikinsa. Bincike ya nuna cewa, amfani da citta na bunkasa garkuwar jikin mutum yadda za ta iya yaki da cuta idan har ta kawo wa jiki farmaki. Hakanan, cittar na taimaka wa mutum saurin murmurewa daga rashin lafiya.
Domin samun wannan fa'ida ta citta, sai ka zuba babban cokali biyu na ruwan citta da aka matse cikin kofi daya na ruwan zafi, sai ka zuba ruwam lemon tsami guda daya da ka matse, sannan ka zuba babban cokali daya na zuma mai kyau. Wannan hadin za ka sha sau biyu a rana, wato safe da kuma yamma kenan.
12. Maganin Ciwon Gabobi
Tun a farkon wannan makala mun bayyana cewa, shekaru aru-aru da su ka shuda, al'ummomi daban-daban na duniya ke amfani da citta don maganin ciwon gabobi, to haka al'amarin ya ke har a gobe, ana amfani da citta wajen maganin ciwon gabobi. Saboda citta na da wasu sanadarai da ke hana ciwon gabobi sakamakon aikin karfi ko na gajiya ko kuma wasannin motsa jiki da mutum ya gudanar.
Ɗaya daga cikin binciken da aka wallafa a mujallar 'Journal of Pain' ya gano cewa, mutanen da ke wasannin motsa jiki na yin amfani da hadin da aka sarrafa daga citta don maganin ciwon gabobi, bayan sun kammala wasannin motsa jiki.
13. Maganin Kaikayin Makogwaro Da Toshewar Hanci
A lokacin da mutum ke fama da toshewar hanci ko kaikayin makogwaro sai ya nemi citta ya sarrafa ta don samun sauki, sakamakon yadda bincike ya nuna cewa ta na da wasu muhimman sandarai da ke wannan aikin.
Yadda zai yi shine, ya hada shayi da danyar citta bayan ya kirba ko dandaka cittar, sai ya zuba ruwan lemon tsami guda daya da ya matse, sannan ya zuba zuma cokali daya ya sha.
Daga shafin Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci.

Comments
Post a Comment