ILLOLIN WASA DA TSARAICI
ILLOLIN MASTURBATION DA HANYOYIN MAGANCE SU Masturbation ko kuma Istimna'i a Larabce, shi ne wasa da tsaraici don biyawa kai bukatar sha'awar jima'i. Bayan Addinin Musulunci ya haramta Istimna'i wato Masturbation, to kuma yana da illoli da cututtuka da yake haddasawa a jikin mutum. Yana janyo:- 1- Yawan mantuwa. Duk mai wannan aiki zai gamu da yawan mantuwa da shiririta. 2-Yana rage hazaqar kwalwa. Duk karatun da mutum yake ganewa zai dawo ya dena fahimta. 3- Kankancewar gaba da maraina ya koma kamar na yaro karami ko ya tattare ya dinga komawa ciki. 4-Saurin kawowa yayin jima'i. Wani ko minti daya ba ya iya yi, yayin tarawa da iyalinsa sai ya ji ya kawo kuma ba zai iya komawa ba. 5-Ramewa. Mutum zai ta ramewa, komai cin abincinsa da shan magunguna kara kiba. 6-Rashin karfin mazakuta har ta kai in yay aure ba ya iya gamsar da iyalinsa. 7- Mazakutar namiji tana iya karyewa, ya zama kwata-kwata ya dena tashi, sedai ya dinga dan motsawa kadan. 8- 'Kara...