RUWA MAI KAMAR JINI DA MATA SUKE GANI BAYAN GAMA JININ HAILA. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

RUWA MAI KAMAR JINI DA MATA SUKE GANI BAYAN SUN GAMA  HAILA.

  Na samu waɗannan tambayoyi guda biyu a yau, sai na ga ya kamata in ɗan yi bayani koda a taƙaice ne.
   Wannan ruwan mai jaja-jaja da mata suke gani lokacin jinin al'ada ko bayan ɗaukewar jinin al'ada, da larabci ana kiransa 'ƙassatul baibwa'a', ɗaya kenan daga cikin hanyoyin da mace za ta gane jinin hailarta ya ɗauke. 
   Ruwa ne mai kamar jini, saidai shi ruwa ne sosai amma ya canja kala, ya ɗan yi ja. Zuwansa alama ce da ke nuna cewa jinin al'adar mace ya ɗauke, don haka sai ta yi wanka ta ci gaba da ibada. 

     Abinda ke rikita wasu matan shi ne : bayan sun yi wanka sun cigaba da ibada sai wannan ruwan ya sake dawowa, sai wasu su kasa gane cewa shin sai sun sake yin wanka ko kuma ba sai sun sake yin wanka ba?!. Sannan idan suna Azumi shin Azumin ya karye ko yana nan?!.

    To amsa dai ita ce: Dukkan abinda mace ta gani ya fito mata wanda ba jini ba to ba ya ɗaukar hukuncin jini. Sannan shi ma jinin sai ya cika sharaɗan jinin haila ko jinin biƙi sannan hukuncin barin sallah da Azumi suke hawa kan mace.

    Don haka, wannan ruwan da mata suke gani ba ya hana sallah kuma ba ya hana Azumi.

    Na taɓa yin dogon bayani akan jinin haila da hukunce-hukuncensa amma zan dubo shi, na sake yin posting, insha Allahu.

   Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

Comments

Popular Posts