YADDA AKE YIN MAN DARBEJIYA DA KUMA AMFANIN MAN DARBEJIYA. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

YADDA AKE YIN MAN DARBEJIYA DA KUMA AMFANIN MAN DARBEJIYA.

    Za ka iya bin wannan hanya domin yin Man Darbejiya da kanka a gida. 

    Da fari sai ka samu ganyen Darbejiya, zallar ganyen za ka ciccire, banda itacen. A wanke shi sosai a cire datti, a shanya shi a waje mai kyau, cikin inuwa, ya bushe. 
    Sai kuma a samu ƴaƴan Darbejiya tare da ƙwallayen da ke cikinsu, shi ma a wanke sosai, a shanya, ya bushe. 

Daga nan sai haɗa ganyen ga ƴaƴan a daka su ko a niƙa har sun zama gari. 
     A samu tukunya a zuba su aciki sai a zuba ruwa a juya sosai, ya haɗu. Daga nan sai a kunna wuta kaɗan_kaɗan, idan ya fara tafasa sai a zuba Man Zaitun aciki. A bar shi ya cigaba da tafasa, har sai ruwan ya ƙone, ya zama saura man, sai a sauke, a tace. 

   Idan kuma ɗanyen man Darbejiya ake bukata, to kawai bayan an daka sun zama gari sai a samu man Zaitun a zuba aciki, a ajjiye shi tsawon kwana uku zuwa huɗu. Za ka ga man ya koma kore mai ɗaci. 

Man Darbejiya na da matukar amfani ga lafiya da gyaran fata da gashi da magance cututtuka da kashe ƙwayoyin cuta da rigakafin wasu cututtuka.
   Man Darbejiya na warkar da, makero, cin ruwa, garjen giwa, kaikayin fata, ƙarzuwa, da kuma ƙurajen da ke samuwa a sanadin cizon wasu ƙwari.

1- Laushin Fata. 
    Wanda fatar jikinsa ta bushe ko mai neman fatar jikinsa ta yi laushi ya jarraba shafa man Darbejiya ya gani, zai yi mamaki.

2- Man darbejiya na warkarda kunan rana dake ɓata fuska, inda za ka ga mutum fari da shi amma fuskarsa baƙa ko yana baki amma fuskar ta sa ta fi fatar jikinsa dushewa.

3- Man darbejiya na warkarda kuraje masu kaikayi a kan fata da ake ta’allakawa da fungal infection.

4- Man Darbejiya na kare fatar jiki daga kwayoyin cuta iri iri.
  A gauraya da Vaseline a dinga shafawa.

5- Man Darbejiya na maganin Ƙyasbi.

6- Man Darbejiya na maganin pimples da suka mamaye fuskar mace ko namiji.

7- Man Darbejiya na da  inganci musamman ta ɓangaren gyaran gashi, domin yana sa gashi yai baƙi, yana kashe kwayoyin cuta dake kwance a cikin kai musamman ga mata masu jin ƙaiƙayi ko wasu ƙuraje da ke tsira a cikin fatar kai masu ƙaiƙayi ko zafi.

8- Man Darbejiya yana warkar da tsagewar fatar jiki da bushewarta da garjin fata da ma dushewar fata.

9- Man darbejiya na maganin cututtukan baki(mouth infections) kamar wanda ke brush yana ganin jini a hakoransa ko wanda dasashinsa ke kumbura yana masa ciwo.

10- Man ƴaƴan darbejiya na maganin kunar fata a sanadin wuta.

11- Man ƴaƴan Darbejiya  na maganin dandruff (amosani) ga maza da mata.

12- Man ƴaƴan Darbejiya na maganin ƙurajen nan da ake kira na damina.

13- Man ƴaƴan Darbejiya na maganin kaikayin matse matsi a shafa kullum sau biyu.

14- Yana maganin ciwon daji kamar na mama (breast cancer) da (skin cancer) wato kansar fata. 

15- Maganin Kwarkwata. 
     A shafa man Darbejiya, a ɗaure kan bayan tsawon lokacin sai a wanke kan, a sake shafawa. 

    Ana amfani da Man Darbejiya wajen magance cututtukan cikin ciki to amma shansa yana da haɗari, don haka a tuntuɓi masana kafin a sha man Darbejiya.

    Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

Comments

Popular Posts