GAME DA SALLOLIN TAHAJJUDI DA TARAWIHI. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
GAME DA SALLOLIN TAHAJJUDI DA TARAWIHI. * 1- Ya tabbata Annabi (SAW) yana kara kokari na ibada a cikin goman karshe na Ramadhan, kokarin da ba ya yin irinsa a wasu kwanakin. عن عائشة رضي الله عنها قالت: كَانَ رَسُولُ اللَّهِ ﷺ يَجْتَهِدُ فِي رَمضانَ مَالا يَجْتَهِدُ في غَيْرِهِ، وَفِي العَشْرِ الأَوَاخِرِ منْه مَالا يَجْتَهدُ في غَيْرِهِ" رواهُ مسلمٌ. * 2- Asali Allah Ya kwaɗaitar a yi sallar Tahajjudi har ma ya ce ya kusanta Allah Ya tasheka a wani matsayi mai girma. {وَمِنَ اللَّيْلِ فَتَهَجَّدْ بِهِ نَافِلَةً لَكَ } [الإسراء: 79] Tahajjudi shi ne rashin bacci da raya dare da Sallah da Ibada. * 3- Annabi (SAW ) ya kasance yana raya dare da Ibadau a goman karshe kamar yadda ya zo a Hadisin A’isha (SAW ) cikin Bukhari da Muslim. وعَنْهَا رَضَيَ اللَّه عَنْهَا، قَالَتْ: كَانَ رسُول اللَّهِ ﷺ: إِذا دَخَلَ العَشْرُ الأَوَاخِرُ مِنْ رمَضَانَ، أَحْيا اللَّيْلَ، وَأَيْقَظَ أَهْلَه، وجَدَّ وَشَدَّ المِئزرَ متفقٌ عَلَيهِ. * An sunnanta mana yin Jam’i a Sallar...