Posts

Showing posts from October, 2018

AMFANIN ALMISKI

Image
AMFANIN ALMISKI ============== Shi Miski ba tsiro ba ne, ana samar da shi ne daga jikin Barewa, kuma Allah ya fade shi a Alqur‘ani. . Amfanin sa; * Yana maganin dafi kowane iri. . * Yana kara karfin jiki. . * Yana maganin hawan jini idan an sheka. . * Yana maganin Aljanu, ya kan ma iya kashe Aljani idan an hada shi da Za‘afaran ana shafawa, ana kuma iya zuba shi a garwashi a dinga hayaki. . *yana maganin warin gaba idan ana shafawa. . *yana maganin namijin dare. . *yana taimakawa masu masu matsalar haihuwa idan suna matsi da shi bayan gsma al'ada. . . Akwai jan Miski akwai baki kuma akwai farin Almiski akwai kuma miski na ruwa. . . Daga shafin Bashir Halilu Tarbiyyah Islamiyyah. . bashirhalilu1989@gmailcom. whatsApp 08162600700

AMFANIN ZA'AFARAN GA LAFIYAR AL'UMA

Image
AMFANIN ZA'AFARAN ================== Ga lafiyar al'umma. . . Daga cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah. Masu yin Ruq'yah da harhada Magungunan Musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846. . Za'afaran wata ciyawa ce ko kuma tsiro mai dauke da launi mai abin sha'awa. Ana amfani da shi wajen sinadarin girki kuma yana maganin cututtuka da dama. An fara noman Za'afaran ne a wajejen Greece. Sannan akay Safararsa zuwa Yammacin Amurka da kuma kasashenmu na Afrika. . . Za'afaran yana maganin cututtuka kamar: .    ★Zubewar Gashi. Shafa Man Za'afaran a fatar kai yana maganin sanqo. Hada Za'afaran da madara a shafa a kai yana maganin zubewar gashi kuma yana kara yawan gashi. . .     ★Gyaran Fuska Hada Za'afaran da madara a shafa a fuska a hankali amma a kaucewa ido. A bar shi tsawon minti goma sha biyar sannan a wanke da ruwa yana sa fuska tay kyau da sheqi. Ana yin wannan hadin sau daya a sati. . .     ★Matsalolin fata. A...

MAGAGIN BACCI

Image
MAGAGIN BACCI Da abubuwan da suke kawoshi da kuma yadda ake maganinsa. Daga cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah, masu yin Ruq'yah da harhada magungunan musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846. Ma'anar Magagin Bacci itace:- Mutum ya dinga magana ko tafiya ko yin wani aiki da jikinsa, alokacin da yake cikin bacci, ba tare da ya farka ba. Yawanci dai Magagi ba ya wuce mintuna biyar zuwa sha biyar yake sakin mutane. Magagin bacci, kamar yadda binciken zamani ya nuna, yana da alaqa da matsalar Dannau (karanta cikakken bayani akan Dannau acikin wannan shudin rubutun    http://bashirhalilu.blogspot.com/2018/04/dannau-dannau-lokacin-bacci-aljani-mai.html  ) inda binciken ya nuna cewa, a yayinda mutum yake bacci, to kwakwalwarsa da gangar jikinsa dukkansu suna hutawa ne, idan ya tashi farkawa kuma sai su farka gaba daya.      To idan aka samu matsala, kwakwalwar mutum ta farka, gangar jikinsa kuma bata farka ba, sai mutum ya ji ya dawo cikin hanka...

JINNUL ASHIQ. ALJANI MAI SADUWA DA MATAN MUTANE.

Image
JINNUL ASHIQ Aljani mai hana aure ko mai kwanciya da matan mutane ﺟﻦ ﺍﻟﻌﺎﺷﻖ Idan aka ce Jinnul Ashiq na nufin Aljanin da ke zuwa da daddare yana saduwa da matan mutane, ana kuma samun Aljana mai zuwa da dadddare ta dinga saduwa da namiji. Daga shafin Tarbiyyah Islamiyyah, masu yin Ruq'yah da harahada magungunan musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846. . Su irin wadannan Aljanu suna aurar mace ne ta yadda za su dinga kwanciya da ita a duk lokacin da suka ga dama suna kuma kokarin hana ta aure, in kuma tana da auren sai su dinga kokarin kashe mata shi. Su na kuma kokarin hana mace samun ciki, ko kuma in ta samun cikin sai su zubar mata da shi. Sukan ma biyo yaron da matar ta haifa, ya zamo tun daga haifar sa za a ga alamun jinnu a tare da shi. Irin wannan nau'in Aljani shi muke kira JINNUL ASHIQ ﺟﻦ ﺍﻟﻌﺎﺷﻖ Wani lokacin irin wannan Aljanu suna shiga jikin mace ko n...

ALJANAR JARIRAI. UMMUL ATFAL. ALJANA MAI SHIGA JIKIN KANANAN YARA

Image
أم الأطفال    UMMUL ATFAL ====================== . . Aljanar Jarirai. . Aljana mai shiga jikin Qananan yara. .                                   Ummul Atfaal                ﺍﻡ ﺍﻻﻃﻔﺎﻝ                    ko kuma Inna-Uwa a Hausance . .Daga cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah masu yin Ruq'yah da harhada Magungunan musulunci 08162600700. .                                ...