SIHIRIN SAKAWA MUTUM RASHIN LAFIYA SIHRUL MARADH (سِحْرُ الْمَرَضِ) Daga shafin Dr. Bashir Halilu. Lambar waya 08134434846.
Dr. Khalid bin Abdur-Rahman Al-Juraishi ya kawo bayani akan wannan nau'in sihiri a cikin littafinsa الحذر من السحر inda ya yi amfani da sunan سحر المرض أو الإمراض wato sihirin cuta ko sihirin jawo cuta. Haka nan a cikin littafin «الصارم البتار في التصدي للسحرة الأشرار» na Shaikh Waheed bin Abdus-Salam Baali, an kawo bayani a kan wannan nau'in sihiri da ake kira Sihrul Maradh (سِحْرُ الْمَرَضِ), wato sihirin cuta. Wannan suna 'Suhrul Maradh', yana nufin wani nau'in sihiri da ake yin sa domin a cutar da mutum ta fuskar lafiyar jikinsa, kamar haifar masa da ciwo ko wata matsala a wani sashe na jikinsa. Abu ne sanane cewa Shaiɗan ko Aljani na iya sakawa mutum cuta a jikinsa, saidai hakan zai iya faruwa ta hanyar sihiri ko ba ta hanyar sihiri ba, sannan cutar tana iya tasiri idan Allah Ya so. A cikin Alkur'ani mai girma, suratu Sād, ayah ta 41,...