HIJIRAR FARKO ZUWA HABASHA DA KUMA MUSULUNTAR NAJJASHI SARKIN HABASHA
Daga shafin Bashir Halilu. Mallam Ibnu Kasir ya kawo acikin littafin Al-Bidāyah wan-Nihāyah cewa: Lokacin da azabar da Musulmai suka fuskanta a Makka ta yi tsanani daga kuraishawa, Manzon Allah ﷺ ya ba su shawarar su koma ƙasar Habasha (wato Ethiopia) ya ce: "A can akwai sarki wanda ba a zaluntar kowa a ƙasarsa, kuma ƙasarsa ƙasar gaskiya ce, ku tafi har sai Allah Ya kawo muku mafita.” Sai wasu daga cikin Sahabbai suka yi hijira zuwa can, cikinsu har da Ja’afar ɗan Abī Ɗalib da Abdullahi bn Mas’ūd da Zubayr binil ‘Awwām da wasu daga cikin musulman farko. Da Ƙuraishawa suka ga cewa Musulman sun samu mafaka a Habasha, sai su ka aika da wakilai guda biyu: ’Amru binil-‘Āṣ da ’Abdullāhi bin Abī Rabī’ata, su ka ɗauki kyaututtuka masu yawa domin su ba sarkin Habasha da manyan fadawansa don su dawo musu da Musulman nan zuwa Makkah domin su cigaba da azabtar da su. Ko da su ka isa garin Habasha sai s...