Posts

Showing posts with the label So

MUTANE GOMA WAƊANDA ALLAH BA YA SON SU

Image
Allah Maɗaukakin Sarki Ya ambaci waɗansu halaye a cikin Alƙur'ani, inda Ya bayyana ƙarara cewa ba Ya son mutanen da ke aikata su. Yi ƙoƙari kada ka zama ɗaya daga cikinsu.    Daga Shafin Bashir Halilu. 1. الكافرون KAFURAI > ﴿إِنَّ اللَّهَ لا يُحِبُّ الْكافِرِينَ﴾ [آل عمران: 32] Haƙiƙa Allah ba Ya son kafurai.     Ayah ta 32, suratun Nisa'i 2. الظالمون AZZALUMAI  > ﴿وَاللَّهُ لا يُحِبُّ الظَّالِمِينَ﴾ [آل عمران: 57، 140] Kuma Allah ba Ya son azzalumai.    Suratu Ali Imran ayah ta 140 da kuma ta 157.  3. المعتدون MASU ƘETARE IYAKA KO KARYA DOKOKI. > ﴿إِنَّ اللَّهَ لا يُحِبُّ الْمُعْتَدِينَ﴾ [البقرة: 190] Haƙiƙa Allah Ba ya son masu ƙetare iyaka (masu kawo tashin hankali acikin jama'a).  4. المفسدون MAƁARNATA > ﴿وَاللَّهُ لا يُحِبُّ الْفَسَادَ﴾ [البقرة: 205] ﴿إِنَّهُ لا يُحِبُّ الْمُفْسِدِينَ﴾ [القصص: 77] Kuma Allah ba Ya son ɓarna.  Suratul Baƙarah, ayah ta 205.     Haƙiƙa Shi (Allah) ba Ya son maɓarnata. ...