MAGANIN WASUWASI. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

MAGANIN WASU-WASI

Wasu-wasi ya kan hana mutum yin ibada cikin nutsuwa ko yin harkoki cikin kwanciyar hankali.

Da akwai wasu-wasi mai alaqa da lalura irinta Aljanu, wani lokacin kuma wasu matsaloli ne daban suke kawo shi amma ga 
YADDA MUTUM ZAI GANE YANA DA SHAIDANI
MAI SA WASU-WASI

1) Haka kawai mutum ya dinga jin tsoro.
Sai ya zamto mutum yana jin tsoro in ya ganshi shi kadai ko kuma idan ya shiga duhu.
Wani lokaci ko yaya aka dan motsa wani abu ko aka fadi wata magana sai mutum ya tsorata.

2) Mutum ya dinga tunanin ya kusa mutuwa.
Ko mutum ya ji kamar an tashi kiyama. Wani
lokaci sai mutum ya dinga ji kamar wani mummunan abu ne zai same shi.

3) Mutum ya dinga tunanin kamar ba shi da
tsarki. Ko ya dinga tunanin alwalarsa ta
karye. Ko ya ji kamar ya yi tusa ko kuma wani
abu ya fita daga gabansa.

4) Yawan tsarguwa.
Shi ne da an yi wani abu
sai mutum ya dauka da shi ake. Misali da
ance anyi sata sai mutum ya ji kamar shi ake zargi
Ko kuma idan an kalleka sai ka ji kamar da
wata manufa ake kallonka.

5) Kin mu'amala da mutane.
Mutum zai ji sam
be yarda da kowa ba. Ko ya dauka duk
mutane ba su yarda da shi ba. Don haka zai ji
ba shi da sakewa a cikin mutane.

6) Ramewa haka kawai.
Saboda yawan
tunane-tunanen da mutum ya ke, haka kawai
sai a ga yana ramewa. Kuma koda zai sha
maganin kiba ba zai masa wani amfani ba.

7) Mutum zai dinga jin kamar idan ya fito
waje kama shi za a yi.
Wani ma zai ji kamar
koda kayan sana'a ya yi kamar ba za a siya
ba.

8) Rashin samun bacci.
Mutm zai kwanta
amma sai bacci ya ki daukarsa. Sai dai mutum
yay ta juyi yana tunane-tunane.

MAGANIN WASU-WASI

1- Zama da Alwala.
.
2- Karanta Falaqi da Nasi.
.
3- Yawan karanta isti'aza.
.
Yin addu'o'in safiya da maraice.       
                  
Da akwai kuma magunguna da ake hadawa don magance wasu-wasi mai alaqa da Shaidanu, za kuma a iya yi ma ka rukiyyah idan nau'in Aljanin wanda ake yiwa rukiyyah ne. 

Daga shafin Bashir Halilu mai ruq'yah da harhada magunguna na Musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

Comments

Popular Posts