FALALAR DAREN LAILATUL ƘADRI DA KUMA ABUBUWAN DA AKE SO A YI A CIKINSA. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
DAGA CIKIN FALALAR DAREN LAILATUL ƘADRI.
1- Acikin Daren Lailatul Ƙadri aka saukar da Alƙur'ani. Allah Maɗaukakin Sarki Yana cewa:
(إِنَّا أَنْزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةِ الْقَدْرِ)
2- Allah Maɗaukakin Sarki Ya kira daren Lailatul Ƙadri da suna dare mai albarka. Allah Ya ce:
(إِنَّا أَنزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةٍ مُّبَارَكَةٍ)
3- A daren Lailatul Ƙadri ake ƙaddara dukkan abinda zai faru a duniya sannan a saukar da shi daga lauhul mahfuzu zuwa Mala'ikun da za su zartar da aikin. Dukkan abubuwan da za su faru a duniya na ayyukan bayi kamar arziki da haihuwa da mutuwa da dai sauransu. Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:
(فِيهَا يُفْرَقُ كُلُّ أَمْرٍ حَكِيمٍ)
4- Ibada acikin daren lailatal qadri ana ninninka ladanta da falalarta. Ta yadda daren shi kaɗai ya fi wata dubu alkhairi. Inda Allah Maɗaukakin Sarki Ya ke cewa :
(لَيْلَةُ الْقَدْرِ خَيْرٌ مِّنْ أَلْفِ شَهْرٍ)
5- Daren lailatul Ƙadri dare ne na salama da aminci, ta yadda Allah Ke saukar da Mala'ikunSa zuwa duniya da alkhairi da rahma, dare ne mai aminci har zuwa ketowar alfijir. Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:
(سَلَامٌ هِيَ حَتَّى مَطْلَعِ الْفَجْرِ)
6- Lailatul Ƙadri dare ne na gafartawa bayi zunubansu. Manzon Allah (SAW) ya ce
(مَن قَامَ لَيْلَةَ القَدْرِ إيمَانًا واحْتِسَابًا، غُفِرَ له ما تَقَدَّمَ مِن ذَنْبِهِ)
Ma'ana: "Wanda ya tsaya (yai ibada) a daren Lailatul Ƙadri yana mai imani da Allah da neman lada wajen Allah za a gafarta masa abinda ya wuce na zunubansa".
ABINDA AKA FI SO MUTUM YA YI DON NEMAN DACEWA DA DAREN LAILATUL ƘADRI.
1- Sallolin Nafila.
2- Karatun Alƙur'ani.
3- Sauran zikirai, kamar Hailala, hamdala, tasbihi, istigfari, salatin Annabi (SAW) da sauran zikirai.
4- Addu'o'i na alkhairi.
Da sauran ayyukan alkhairi.
Allah Ya sa mu dace.
Comments
Post a Comment