SARIƘUL JINNI. ALJANI MAI SATAR KUƊI DA KAYAN MUTANE. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

SARIQUL JINNI سارق الجن 

`Barawon Aljani.

Aljanu masu satar kayan mutane.

Galibin wadannan Aljanu a gidajen mutane suke zaune da kuma kasuwanni.

Suna iya satarwa mutane kudi, abinci da kuma sauran kayan amfani.

Waddannan Aljanu wato Sariqul Jinni sukan iya sato kayan mutane su kawo gidanka su ajjiye ko su ajjiye a aljihun mutum ko cikin kayansa.
Sannan suna aron kayan mutane daga baya su dawo musu da shi.

Sariqul Jinni suna da hadari sosai domin suna hada gaba da zargi a tsakanin mutane.

Hakanan suna da taurin kai sosai, ba sa rabuwa da mutum ko gidan mutane ta dadi.

Irin wadannan Aljanu su ne Bokaye masu buga kudi suke yin amfani da su  ta hanyar saka su su sato musu kudaden jama'a.

Ashararain mutane suna iya yin Sihiri su tura Sariqul Jinni jikin wani mutum ko gidan wani mutum don su dinga satar masa dukiya suna 6atar masa.

Hakai dai Bokaye suna iya tura su jikin mutum,  sai mutum ya zama tantirin 6arawo kuma yana yin satar ne ba a son ransa ba. Suna kuma iya shiga jikin mutum ta hanyar tsautsayi.

Sariqul Jinni sun dade a duniya. Domin Allah madaukakin Sarki ya yi bayani akan Aljanu masu satar ji a cikin Suratul Hijri da Suratus Saffati da Suratul Jinni da dai wasu surori na Alqur'ani.

SAHABIN MANZON ALLAH صلى الله عليه وسلم 
YA KAMA `BARAWON ALJANI

Aba Hurairata (RA) ya kama Sariqul Jinni hannu da hannu.

An kar6o daga Aba Hurairata Allah ya kara yarda a gareshi, ya ce " Manzzon Allah صلى الله عليه وسلم
Ya wakiltani in kula da zakkar watan Azumin Ramadana. Sai ga wani ya zo yana satar abincin (da nake gadi).

Sai na kama shi, na ce Sai na kai ka wajen Manzon Allah صلى الله عليه وسلم.

Sai ya ce min "WAllahi ni mabukaci ne kuma ina da iyali da yawa ga kuma tsananin bukata"

Sai na rabu da shi.

Da gari ya waye sai Manzon Allah صلى الله عليه وسلم 
Ya ce "Ya kukai da bakonka na jiya?"

Sai na ce Ya Ma'aikin Allah, ya koka min tsananin bukata da kuma yawan iyali. Sai na tausaya masa na kyale shi.

Sai Manzon Allah صلى الله عليه وسلم 
Ya ce "Karya yake kuma zai dawo"

Saboda haka sai nay tarkonsa.

Sai kuwa gashi ya dawo yana satar abincin. Sai na kama shi, na ce to wAllahi sai na kai ka wajen Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
Domin karo uku kenan ina kama ka. Se kay rantsuwa ba za ka dawo ba sai kuma ka dawo.

Sai ya ce "To ka kyale ni se in koya maka wasu kalmomi wadanda Allah zai sa ka amfana da su".

Sai na ce Wadanne ne?

Sai ya ce "Idan ka je wajen kwanciyarka, ka karanta Ayatal Kursiyyu har karshen ayar. To  Akwai me gadi da Allah zai saka maka kuma Shaidan ba zai iya kusantarkaba har sai ka wayi gari".

(Da Manzon Allah صلى الله علي وسلم 
Ya ji haka sai ya ce "Amma fa shi (wannan mai zuwar maka da daddaren) makaryaci ne, sai dai gaskiya ya gaya maka. Ya Aba Hurairata ka san ko da wa kake gamuwa har sau ukun nan?"

Sai na ce A'a.
Sai ya ce "Shaidan ne"

Daga wannan hadisi za mu fahimci cewa lallai Shaidanun Aljanu suna zuwa su saci kayan mutane.
YADDA MUTUM ZAI GANE SARIQUL JINNI YA SHAFE SHI.

Kalli bidiyoyinmu acikin wannan shuɗin rubutun
https://www.youtube.com/@bashirhalilutv
Lambar waya 08162600700, 08134434846. 

1- yawan 6atan kudi da kayan amfani kuma a rasa wanda ya dauka.

2- yanzunnan za ka ‘kirga kudi ka sa a aljihu ko wani abu amma in ka sake ‘kirgawa sai ka ga sun ragu.

3- duk irin 6oyewar da kay wa kudin ka sai ka ga an ta6a ma ka ko an dauke gaba daya.

4- zaka dinga yawan ganin an yi ma kaca-kaca dakayan ka, an yi ma bincike kuma ba ka san kowaye ba.

5- za ka ajjiye kayanka ko kudi sai ka ga an canja musu waje.

6- wani abinka zai 6ata, sai ka gaji da nema kaha‘kura sai kuma ka gan shi daga baya .

7- za ka ji kana da sha‘awar ka dauki kudin da bana ka ba ko wasu kaya koda kuwa ba abinda za kai da shi.

8- idan yaro yana da Sariqul jinni zai dinga yawan dauke-dauke kayan mutane da kudinsu kuma in an caje shi ba za a ga komai ba.

9- Za a dinga ganin yaro da kudi, in an tambaye shi a ina ya samu zai ce shi ma bai sani ba domin Aljanin ne ya sato ya saka masa.

10- Mai Sariqul jinni za a dinga yawan ‘kala masasatar da bai ji ba bai gani ba: don kuwa Aljanin nezai yi satar sai a ce kai ne.

11-Mutum zai ajjiye kudinsa amma sai ya tashi dauka sai ya ga sun zama takardu ko qasa ko kuma ganye.

SARIQUL JINNI TA HANYAR SIHIRI 

Wani lokacin ana iya hada baki da Boka ya tura wa mutum Sariqul jinni don ya dinga yi ma sa 6arna acikin dukiyar sa.Shi kuma bayan alamomin da mu ka ambata asama to zai dinga fama da wadannan:-

1- karyewar kudin mutane a ka.

2- zai kasa kaya ai ta siyan na kowa amma a ‘kikallon na sa (don kuwa Aljanin ne zai lullu6e ma kayan ba wanda zai gan su)

3- ta6ar6arewar harkar ciniki.

4- kudi za su lalace amma ka rasa abinda ka siya dasu.

5- fama da matsanancin ciwon kai musamman dab da Magriba.

6-yawan faduwar gaba.

7- 6acin rai mara dalili.

7- za ka dinga mafarkin ana bin ka a guje ko anakokawa da kai.

8- za ka ji sam ba ka son fita kasuwa.

9- in kana kasuwa sai hankalin ka yai ta tashi,amma da ka dawo gida ko ka tafi wani wajen shikenan sai ka dena.

10-fada da abokan ciniki

11- za ka ji kamar ana kiran sunan ka amma ba kaga kowa ba.

12- ko wani ka ba wa kudi indai na ka ne sai an yima sa sata.

Daga shafin Bashir Halilu mai Rukiyyah da bayarda magunguna na Musulunci dana gargajiya. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

Kalli bidiyoyinmu acikin wannan shudin rubutun
https://www.youtube.com/@bashirhalilutv

Comments

Popular Posts