MAGUNGUNAN GARGAJIYA DA SUKE ƘARAWA MUTUM JINI A JIKINSA Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

MAGUNGUNAN DA SUKE KARAWA DAN'ADAM JINI  A JIKINSA. 

Ga jerin sunayen wadansu magungunan gargajiya guda goma sha bakwai, wadanda suke karawa mutum yawan jini ajikinsa. Musamman saboda mata masu ciki da mutanen da suka zubar da jini yayin hatsari da kuma sauran masu dauke da lalurar da ke konar da jini daga jikin mutum. Haka nan masu neman inganta lafiyarsu ta hanyar jini, su ma za su iya amfani da su don kara yawan jini a cikin jiki. 
1- Ganyen Auduga. 

2- Ganyen So6arodo, ko a ce Yakuwa. 

3- Ganyen Zamarke, ana kuma kiransa Kalambu. 

4- Saiwar Gwandar_daji, tana kara yawan jini kuma tana rage hawan jini. 

5- Giginya. Wato tsokar Giginya din. 

6- Saiwar Kargo. 

7- Saiwar Hanjiri. 

8- Ganyen Geza. 

9- 'Ya'yan Kanya. 

10- Saiwar Tsa. 

11- Saiwar Qirya. 

12- Sassaken `Baure. 

13- Saiwar Goruba. 

14- Saiwar Tsaure. 

15- Qamsuwa. Baki dayanta ake amfani da ita. 

16- Goga_masu. Shi ma baki dayansa ake amfani da shi,  don kara jini. 

17- Sassaken Kukkuki. 

★ Dukkan wadannan tsirrai da itatuwa da mu ka ambata ana tafasawa ne, idan ya huce sai a sha,  kana iya katawa da zuma ko kuma ka saka jar kanwa kadan aciki, in kana gudun ya 6ata maka ciki. Za ka iya hada biyu ko uku daga cikinsu, ka dinga sha, ba lallai sai ka samu duka ba. Zai fi kyau ka yi amfani da abinda ka sanshi, cikin abubuwan da mu ka ambata,  maimakin neman wanda ba ka sani ba ko wanda zai ba ka wahala. 

Daga shafin Bashir Halilu. 
 Lambar waya 08162600700, 08134434846.

Comments

Popular Posts