Posts

Showing posts with the label haila

SIHIRIN SAKAWA MACE ZUBAR JINI WATO SIHRUN NAZIYF (سحر النزيف) Daga shafin Dr. Bashir Halilu. Lambar waya 08134434846.

Image
        Acikin Littafin Sunan Abī Dāwūd, hadisi na 287 da  Jāmi‘ut-Tirmidhī, hadisi na 128 da Sunan Ibn Mājah, hadisi na 627, an ruwaito hadisi mai tsawo wanda Sheikh Nasirud Dinil Albaniya ya inganta shi cewa:       An karɓo daga Hamnah 'yar Jahsh رضي الله عنها, ta ce:        “Na kasance ina fama da zubar jini mai yawa da tsanani. Sai na je wurin Annabi ﷺ domin neman fatawa da bayyana masa halin da nake ciki. Na same shi a gidan 'yar uwata Zainab bint Jahsh.      Sai na ce: Ya Manzon Allah, ina fama da zubar jini mai yawa da tsanani. Me kake gani game da wannan halin? Domin ya hana ni yin sallah da azumi. Sai ya ce: ‘Zan ba ki shawarar amfani da auduga, domin tana taimakawa wajen tsayar da jini.’ Ta ce: ‘Jinin ya fi haka yawa.’ Ya ce: ‘To, ki ɗaure wani kyalle domin riƙe jinin.’ Ta ce: ‘Jinin ya fi haka yawa; yana zuba sosai.’     Sai ya ce: ‘Zan umarce ki da abubuwa biyu; duk wanda kika aikata daga ci...

CUTUTTUKAN MATA DA MAGUNGUNANSU

1- CIWON NONO 2- GOYON CIKI 3- JININ HAILA 4- RASHIN SHA'AWA 5- ILLOLIN MASTURBATION 6- MAGUNGUNAN GARGAJIYA 7- MAGUNGUNAN ASIBITI CIWON NONO GA MATA. Wato Sanqaran Mama ko kuma Kansar mama. MA'ANAR ciwon nono shi ne samuwar wasu kwayoyin cuta acikin nonon mace, wandanda ke haddasa ciwo da canja yanayin nonon mace ko ya lalata shi gaba daya. Ciwon nono wani lokacin yana janyo ru6ewar nono ko yay sanadin a yanke shi gaba daya. YADDA AKE DAUKAR CIWON Abubuwan da ke kawowa mata ciwon nono. 1- Shekaru ko tsufa.     Idan mace shekarunta suka dan fara yawa, to yana da kyau ta fara daukar matakan kariya daga ciwon nono. 2- Sinadarin 'iyistirogen', idan yay yawa ajikin mace. 3- Fara jinin al'ada kafin mace ta kai shekaru sha biyu, za ta iya gamuwa da ciwon nono daga baya. 4- Mace ta zarce shekaru hamsin da biyar tana jinin al'ada, shi ma zai iya janyo mata ciwon nono. 5- Rashin haihuwa. Matan da sam ba su haihu ba, har su ka wuce shekaru talatin, za su...

ASIRIN HANA HAIHAUWA

ASIRIN HANA HAIHUWA Abu ne sananne cewa akan iya yiwa namiji ko mace sihiri,  domin ahana mutum haihuwa,  ko mace ta dinga yawan yin 6arin ciki,  da dai sauransu. A wannan lokaci za muyi bayani ne insha Allahu akan alamomin da mutum zai gane cewa matsalar haihuwarsa tana da alaqa ne da sihiri ko jinnu ko kuma ba ta da alaqa da su. Kafin nan,  ga wadansu dalilai na dabi'a,  wadanda suke hana daukar ciki,  koda kuwa babu asiri ko Aljani a tare da mutum. ABUBUWAN DA KE HANA SAMUN CIKI 1- ‘Kan‘kantar gaban namiji,  idan ya kasance ba ya iya kaiwa har bakin mahaifarta. 2- ‘Karancin ruwan namiji, ta yadda ba shi yawan da zai iya gangarawa har inda ake so ya je. 3- Fitar jinin haila mai yawan gaske,  wanda kan iya wanko abinda ke cikin mahaifar. 4- In mace tana rub-da-ciki bayan gama saduwa,  hakan zai sa dukkan abinda mijinta ya zuba mata ya dawo,  ba zai shiga mahaifarta ba. 7- Damuwa mai tsanani ko rashin kwanciyar...

MATSALOLIN MATA DA MAGUNGUNANSU

Image
★ JININ HAILA DA YADDA AKE BAMBANCE SHI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA. ★CIWON SANYI NA MATA DA MAZA DA YADDA AKE MAGUNGUNANSA. ★MATSALOLIN DA SUKE FARUWA BAYAN ZUBAR DA CIKI KO 6ARIN CIKI. Daga cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah, masu yin Rukiyyah da harhada magungunan musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846. ASALIN JININ HAILA 1- Datti ne da ke cikin mahaifar mace, shi ne a duk wata ake wanko mata shi yana fitowa. . 2- Kwan haihuwa ne na mace yake saukowa, idan bai samu kwan namiji sun samar da abin halitta ba sai ya lalace ya ru6e, daga nan sai a wanko shi ya fito waje.                   Mace tana fara haila ne lokacinda ta balaga. Mata kan iya fara haila daga shekara tara ko sama ko kasa da haka, ya danganta ne da irin abincin da take ci da kuma yanayin wajen da ta ke rayuwa. Wasu suna daina haila da wuri idan sun fara tsufa, wasu kuma suna dadewa ba su daina ba. Saidai daukewar...