YADDA AKA YI WA MANZON ALLAH (SAW) SIHIRI. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

SHIN AN YIWA MANZON ALLAH (SAW) SIHIRI? KUMA YA KAMA SHI?. 

An karɓo daga Nana A'isha Allah Ya ƙara yarda a gareta, ta ce " Manzon Allah (SAW) ya yi rashin lafiya mai tsanani. Har ta kasance sai ya dinga ganin kamar ya aikata wani abu alhali kuma
be aikata ba.

  Ta ce wata rana yana dakina da daddare, yana ta addu'a, Sai ya kwalla min kira ya ce "Albishirinki
ya A'isha, Allah ya sanar da ni abinda ke damu
na"

    Ya ce "Mala'iku biyu ne suka zo min, daya ya
tsaya a saitin kaina, dayan kuma a saitin kafa ta.
    Sai na saitin kafar tawa ya ce da na saitin kan
nawa "Me yake damun wannan mutumin ne? "

   Sai ya ce masa "An yi masa tsibbu ne"

 Sai ya ce "Meye tsibbu? "

Sai ya ce "Sihiri kenan"

Sai ya kuma ce masa "Wa yay masa sihirin? "

  Sai ya ce " Wani Bayahude ne mai suna Labiydu
binil A'asam, daga qabilar Baniy Zariyqin.

  Sai ya sake ce masa " To yanzu ina (aka binne)
asirin? "

Sai ya ce "A cikin rijiyar Zarawana."

  Daga nan sai Manzon Allah (SAW) ya aika Ammar bin Yasir da wasu mutane, su ka je rijiyar. Sai suka shiga cikinta, ruwan rijiyar gaba ďaya ya koma ja saboda bala'in sihiri. Su ka kwashe ruwan rijiyar, sai suka samu an danne asirin ne da wani katon dutse. Suka dauke dutsen sannan suka fito
da Kullin sihirin.

Da suka kawo wa Manzon Allah (SAW) sai ya warware shi, sai ga shi ashe an hada shi ne da
hudar ÿaÿan dabino namiji, masu kama da kan shaidanu. An yi qulle-qulle ne har guda goma sha daya.

Sai Manzon Allah (SAW) ya karanta surorin Falaƙi da Nasi. Falaƙi aya biyar Nãsi aya
shida, goma sha daya kenan. In yakaranta duk aya daya sai ya tofa a qulli daya, sai qullin ya kwance da kansa, har dai ya gama gaba daya. Daga nan sai aka qona layoyin aka binne. Sai Manzon Allah (SAW) ya samu lafiya, kamar bai ta6a yin cuta ba.

Wannan Hadisi na Nana A'isha (RA) ya zo da ruwayoyi mai son ganin wadannan Hadisai ka iya duba Littafin Šahiyhul Bukhãriy, Kitãbuɗ ɗubbi, Bãbus sihri, hadisi mai lamba ta 5763.

Sauran ɓangarorinsa kuma :- 5766, 5765, 3268,
3175.

Tuhfah:- 16928, 17022, 17134, 17145.

Kuma wannan hujja ce mai karfi da ke nuna cewa ana yin sihiri don a cutar da mutum. Sannan
babban darasi ne da ke nuna cewa ko kai wanene, komai girmanka, komai tsarkin ka komai
matsayinka agun Allah za a iya yi ma Asiri kuma
ya kama ka in Allah Ya so.  Sannan hujja ce da ke nuna cewa lallai ana iya karya sihiri bayan an yi shi kuma wanda akay wa ya samu lafiya.
     Na taɓa yin bayani akan 'MA'ANAR SIHIRI DAGA TAFSIRIN WATTABA'UW', insha Allahu zan dubo shi na sake yin posting domin ganin fadin Allah da Manzonsa da fassara Sahabbai da kuma wasu Malamai akan Sihiri da yadda ake yinsa da kuma matsayinsa a addinin Musulunci.

   Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

Comments

Popular Posts