AMFANIN KANKANA WAJEN ƘARA LAFIYA. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

AMFANIN KANKANA GA JIKIN DAN ADAM
Kankana ta fi amfani ne a lokacin da ta nuna sosai don masana sun ce sinadaran nunannar ya fi taruwa sosai musamman beta-carotene dake cunkushe a cikin jan tozon nan wanda ke matukar taimakawa idanu. 
         Zakin cikinta kuma na ba mutum karfi, tana kuma karawa jiki ruwa.

- Gyaram fatar jiki. 
  Nunanniyar kankana na taimakawa fata saboda
sinadarin lycopene dinta.

- Ƙarfin maza
    Sinadarin arginine dake cikinta na kara yawan
nitric oxide dake karawa namiji karfin gaba.

- Ciwon zuciya da hawan jini. 
    Nitric oxide da wasu sinadaren kankana na
taimakon masu ciwon zuciya da hawan jini.

- Samun bacci. 
   Tana haifar da samuwar wadataccen barci.

- Karin jini
   Sinadarin vitamin C dinta na taimako wajen
maganin cututtuka da dama.

-Cutar kansa da ciwon Ƙoda
     Kankana tana maganin ciwon daji kala-kala, da kuma ciwon koda.

- Kara Karfin jiki
    Tana da sinadarai masu kara karfin kashi
(bone) da kuma maganin kumburin jiki musamman gabban jiki (joints).

Daga shafin  Bashir Halilu Lambar waya 08162600700, 08134434846.

Comments

Popular Posts