AMFANIN MAN KAƊANYA. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
AMFANIN MAN KAƊANYA
Yadda za a magance matsalolin fata ta hanyar amfani da man kaɗanya.
Man Kaɗanya ko man kaɗe, na da matukar amfani a fata, domin yana dauke da sinadarai da dama har da sinadarin bitamin A da E. Wannan man na magance kurajen fuska da gautsin fata da kodewar fuska da kuma kyasbi. Amfani da wannan man na sanya sulbin fata.
Ga kadan daga cikin amfaninsa.
1- Hadin magance ƙyasbi.
A samu man Sandal da man lavender a zuba a cikin man kaɗe sannan a kwaba su sosai sai a samu kwalba a zuba hadin, mayar da wannan mai man shafawa a kullum.
2- Magance fata mai gautsi.
A samu man Kwakwa da man Zaitun da kuma man Almond sannan a zuba a kwalba a kuma zuba man kaɗe a ciki, sai a kwaba da cokali ya kwabu sosai sannan a rika shafawa a jiki.
3- Domin magance bushewar lebba.
A samu Zuma da man Zaitun sai a zuba a kan man Kaɗe a kwaba su sosai. Sai a sa a wuri mai sanyi. Sannan a rika shafawa a baki a kullum za a samu sauki.
4- Domin magance kurajen aski ga maza.
A samu man Rosemary da man kwakwa sannan a zuba a kan man Kaɗe a kwaba, a rika shafawa a kulum bayan an aske gemu. Yana warkar da kurajen da suke fesowa a gemu bayan an yi aski.
5- Magance kaushi da faso.
Mai fama da tsakwar kafafu kamar kaushi da faso, sai wanke ƙafa da daddare, a shafeta da man kaɗanya, a saka kafar a leda lo a nanneɗeta da wani abu. Da safe sai a wanke, a gige kafar, a sake shafawa.
Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
Comments
Post a Comment