Posts

Showing posts with the label Aljanna

AIKIN DA ZAI SHIGAR DA KAI AL-JANNAH KUMA YA HANA KA SHIGA WUTA

Image
Daga shafin Bashir Halilu        An karɓo daga Mu'azu bin Jabal (Allah ya yarda da shi), ya ce:  Na ce: "Ya Manzon Allah, ka sanar da ni wani aiki da zai shigar da ni Aljanna kuma ya nisantar da ni daga Wuta." Sai ya ce: "Lallai ka tambayi abu mai girma! Amma lallai yana da sauƙi ga wanda Allah Ya sauƙaƙa masa:      Ka bauta wa Allah, kada ka haɗa Shi da wani (shirka), kuma ka tsayar da sallah, ka bayar da zakka, ka yi azumin Ramadan, kuma ka yi aikin Hajji zuwa ɗakin Allah (Ka’aba)."     Sai Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ƙara da cewa:      "Shin ba zan sanar da kai ƙofofin alheri ba?    Azumi garkuwa ne (yana kare mutum daga shiga wuta). Sadaka tana cinye zunubi kamar yadda ruwa ya ke kashe wuta, sannan sallar mutum a tsakar dare..." Sai ya karanta: (تَتَجَافَى جُنُوبُهُمْ عَنِ الْمَضَاجِعِ...) har ya kai: (يَعْمَلُونَ) Sai ya ce: "Shin ba zan gaya maka shugaban al'amari ba, da ginshiƙi...