KHUƊUBAR JUMU'A DAGA BAKIN MALLAM BASHIR HALILU
FASSARAR KHUƊUBAR JUMU'ARMU TA RANAR 12/RAMADHAN/1445 = 22/MARCH/2024.
Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya sanya Masallatai su zama gidajensa waɗanda za a ɗaga sauti a ambaci sunansa, a tsarkake shi acikinsu safe da yamma sannan ya Ya sanya Masallatai su zama na Sa ne, don haka Yai umarni kada a kira kowa sai shi.
Kuma ina mai shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai, ba Shi da abokin tarayya, Ubangiji wanda Ya ƙaɗaita da girma da izza da ɗaukaka. Kuma na shaida Annabi Muhammadu (SAW) bawanSa ne kuma ManzonSa ne, ya kwaɗaitar a bisa gina masallatai da tsarkake su daga shirka da sauran aƙidu na ɓata. Ya Allah Ka yi salati a gare shi da iyalan gidansa da Sahabbansa da sauran waɗanda su ka bi tafarkinsa har zuwa ranar tashinsu.
Bayan haka.
Ya ku ƴan uwa, ku sani lallai gina masallatai da tsarkake su da raya su yana daga cikin abinda Ubangijinmu Ya wajabta mana kuma Ya sanya wanda ya aikata haka daga cikin bayinSa shiryayyu.
Allah Mai girma da ɗaukaka Yana cewa "Lallai wanda ke raya masallatan Allah sai wanda yai imani da Allah da ranar lahira kuma ya tsayar da sallah, ya bayar da zakkah kuma ba ya shayin kowa sai Allah, ya kusanta waɗannan su zamo cikin shiryayyu".
Kuma haƙiƙia Allah Ya yi alƙawari da Annabi Ibrahim da Annabi Isma'ila (SAW) cewa su tsarkake ɗakinSa domin masu ɗawafi da masu i'itikafi da masu ruku'i da sujjadah acikinsa.
Acikin Sahihin hadisi, Manzon Allah (SAW) ya ce " Wanda ya ginawa Allah masallaci yana mai neman yardar Allah da shi to Allah Zai gina masa gida makamancinsa a Aljannah"
Ya ku ƴan uwa, daga cikin raya masallatai akwai gina shi, da tsaftace, da sallah acikinsa, da ambaton Allah kamar karatun Alqur'ani da makamantansu, da i'itikafi, da koyar da addini da makamantan haka dadai sauran ayyuka na maslahar musulunci.
Ina roƙon Allah Ya sanya mu cikin masu raya masallatai kuma ya sanya mu cikin shiryayyu.
~~. ~~. ~~. ~~.
Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya wajabta yin Azumi a kanmu kamar yadda Ya wajabta shi akan waɗanda suke kafinmu, tsira da aminci su tabbata ga AnnabinSa wanda Ya aiko da shiriya da addinin gaskiya domin ya rinjayar da shi akan kowane irin addini.
Bayan haka.
Ku sani, daga cikin ayyukan alkhairi a watan Ramadhan ba iya azumi ne kawai ba. Daga cikin ayyukan alkhairi a wannan wata mai albarka akwai yawaita addu'o'i na alkhairi, da i'itikafi, da yawan kyauta, da karatun Alƙur'ani da umara, da barin yi da mutane da gulma da ayyukan saɓo. Sannan ana son ciyar da abinci, da sallolin nafila da sauran ayyukan samun kusanci ga Allah.
Allah Maɗaukakin Sarki Yana cewa
"Lallai Muminai sun rabauta _ har ya zuwa faɗinSa _ Waɗannan su ne masu gado. Waɗanda za su gaje Aljannar Firdausi suna masu dauwama acikinta"
Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce a hadisin Aba Hurairata wanda kuma yana cikin Bukhari da Muslim
" Wanda ya tsaya cikin watan Ramadhana (yai ibada) yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa abinda ya wuce na zunubansa"
Ya Allah Ka sanya mu cikin waɗanda za su tsaya a watan Ramadhana cikin imani da neman lada, kuma Ka gafarta mana abinda mu ka aikata da wanda za mu aikata da wanda mu ka ɓoye da wanda mu ka bayyana da wanda Kai ne ka fi mu sani game da mu, ya Hayyu, Ya Ƙayyumu, Ya Badiy'as samawati wal ardhi, ya Zal jalali wal ikram.
Comments
Post a Comment