GURAREN ZAMAN ALJANU
GURAREN ZAMAN ALJANU ======================= Daga cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah, masu yin Ruqiyyah da harhada Magungunan Musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846 . fb.me/tarbiyyahislamiyyah3 Abu ne mai muhimmanci mutum ya san guraren zaman Aljanu saboda aqalla zai zama ka kiyaye shiga irin wadannan gurare ko kuma ya zama ka yi addu'a idan za ka shige su. Sannan yana da kyau mai Ruqiyyah ko mai bada magani ya san muhallai da kuma guraren zaman Aljanu. Hakan zai taimaka maka sosai ta yadda zaka gane nau'in Aljanin da yake jikin mutum da kuma irin yadda zaka mu'amalanci Aljanin da yadda za kay maganinsa cikin sauqi insha Allahu. . . Za ka samu cewa mafi yawa ko kuma dukkan guraren zaman Aljanu, dama Addini ya yi umarnin mu nisance su in ba da wata lalura ba kuma sunnah ta koyar da addu'o'i yayin mu'amala da wadannan muhallai. . . Mazaunin Aljanu ya danganta da irin addininsu da al'adarsu da kuma ra'ayinsu ko yanayin halittarsu. Musulman ...