AMFANIN GANYEN TAFASA. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
AMFANIN GANYEN TAFASA WAJEN MAGANCE CUTUTTUKA DA KUMA KYAUTATA LAFIYAR JIKI
1- Maganin makanta ko matsalar data shafi gani.
Tafasa na kara lafiyar ido kama daga yara, manya, har zuwa tsofaffi idan ana yin miya da ita ana ci da abinci.
2-Saukaka fitar Bahaya.
Wani bincike da wasu masana tsirran itatuwa suka yi sun tabbatar da cewa Tafasa na maganin wasu cutukan da ke shafar uwar hanji (colon) da kuma taurin bahaya (constipation).
3- Tafasa tana maganin zafin ciki (internal heat) da kuma wanke dattin ciki da ya cushe.
4- Tafasa tana rage kiba. Don haka wannan wata dama ce ga masu tumbi wadanda ke bukatar rage nauyi. Sai a nemi ganyen tafasa a dake tare da gero ayi gumba a dama ayi kunu a dinga sha.
5- Maganin dafin maciji.
Ana amfani da saiwar tafasa idan ta bushe, sai a dake ta koma gari don maganin cizon maciji.
6- Maganin Olsa.
Ana amfani da garin ganyen tafasa dan warkarda gyambon ciki waton ulcers, ta hanyar shan garin tafa da madara ko da ruwa.
7- Tafasa na maganin tsutsotsin ciki(intestinal worms).
8- Tafasa na maganin cutukan fata kamar su ƙarzuwa da makero da kuraje masu kaikayi a jiki.
9- Tafasa na saukarda yawan zafin jiki da hauhawar jini.
10- Kashe ƙwayoyin cuta.
Tafasa na dauke da wani sinadiri mai suna 'chrysophanic acid' da sinadirin 'anthrone' masu kashe kwayar cuta ta fungi.
11- Ganyen Tafasa na inganta lafiyar hanta.(improves liver function).
12- Ana amfani da ganyen tafasa ga yara kanana masu fitarda hakora (childhood teething).
13- Ganyen tafasa na maganin zazzaɓi da ciwon ga6o6in jiki.Sai a nemo ganyen a tafasa ayi suraci da ruwan ko ayi wanka da shi da sanyin safiya ko yamma.
14- Ganyen tafasa na fitar da wasu sinadirran dake gur6ata ciki (toxins) daga jikin mutum.
15- Ƴaƴan tafasa na maganin cutukan sanyi kamar tari da mura musamman ga wadanda ba sa jimirin sauyin yanayi kamar a lokacin sanyi. Ana busar da ƴaƴan tafasa, a soya su, sai a dinga dafawa ana yin shayi da su.
16- Wanda yaci wani abu ko ya sha wani abu dake da alaqa da 'poison' zai iya amfani garin ƴaƴan tafasa inshaAllahu take zai amayar da wannan gubar a cikin lokaci kuma ba zata illata shi ba, daga nan sai a je asibiti.
17- Ganyen tafasa na maganin zazzaɓin Malaria.
18- Ganyen tafasa na warkarda cutukan jini(blood disoders)
19- Ganyen tafasa na maganin cutukan ciki.
20- Warkar da rauni ko ciwo.
Ana amfani da garin ƴaƴan tafasa a markade da mai sai ana shafawa rauni ko wata buguwa ko kuma kunar wuta.
21- Mai fama da basir mai zubar jini (bloody diarrhoea) sai ya tafasa ganyen tafasa ya marmasa gishiri a ruwan ya rinka tsuguno a ciki na mintuna goma ko fiye a duk sanda ya je bahaya.
22- Mai fama da tari sai ya ya markade ganyen a ruwan zafi ya dinga sha.
23- Don magance nauyi ko ciwon mara a lokacin al’ada, sai ayi amfani da tafasa. A dinga tafsawa ana sha.
GARGADI
Mai fama da gudawa ba zai sha tafasa ba.
Mace mai ciki ta kiyayi yawan shan tafasa.
Mai ciwon hanta shi ma ya kiyayi yawan shan tafasa.
Daga shafin Bashir Halilu.
Lambar waya 08162600700, 08134434846.
Comments
Post a Comment