HUKUNCIN SHAN RUBUTU DA DAURA LAYA A ADDININ MUSULUNCI Menene matsayin daura Laya da shan Tofi da shan Rubutu a addinin Musulunci ?. Daga Cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah masu yin Ruq'yah da Harhada magungunan Musulunci . Lambar waya 08162600700, 08134434846 . Abinda ya zo na Hadisan Manzon Allah صلى الله عليه وسلم game da yadda wasu mutane suke amfani da wasu abubuwa da sunan kare kansu daga wani sharri ko kuma janyowa kansu wani amfani. Inda mutane su kanyi amfani da Laya ko Qaho ko Wuri ko Zare ko Dutse, wasu kuma sukan yi Tofe-tofe ajikin wasu abubuwa ko a jikin mutum da sunan magani, yayinda kuma wasu suke rubuta wadansu abubuwa su wanke, su sha. Ko na Alqur'ani ko wanda ba na Alqur'ani ba. Da kuma matsayin yin wanka da ruwan Alqur'ani ko shafe jiki da shi. Da fari dai, ga fadin Allah Madaukakin Sarki a cikin Suratuz Zumar:- بسم ...