Posts

Showing posts with the label wuta

AIKIN DA ZAI SHIGAR DA KAI AL-JANNAH KUMA YA HANA KA SHIGA WUTA

Image
Daga shafin Bashir Halilu        An karɓo daga Mu'azu bin Jabal (Allah ya yarda da shi), ya ce:  Na ce: "Ya Manzon Allah, ka sanar da ni wani aiki da zai shigar da ni Aljanna kuma ya nisantar da ni daga Wuta." Sai ya ce: "Lallai ka tambayi abu mai girma! Amma lallai yana da sauƙi ga wanda Allah Ya sauƙaƙa masa:      Ka bauta wa Allah, kada ka haɗa Shi da wani (shirka), kuma ka tsayar da sallah, ka bayar da zakka, ka yi azumin Ramadan, kuma ka yi aikin Hajji zuwa ɗakin Allah (Ka’aba)."     Sai Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ƙara da cewa:      "Shin ba zan sanar da kai ƙofofin alheri ba?    Azumi garkuwa ne (yana kare mutum daga shiga wuta). Sadaka tana cinye zunubi kamar yadda ruwa ya ke kashe wuta, sannan sallar mutum a tsakar dare..." Sai ya karanta: (تَتَجَافَى جُنُوبُهُمْ عَنِ الْمَضَاجِعِ...) har ya kai: (يَعْمَلُونَ) Sai ya ce: "Shin ba zan gaya maka shugaban al'amari ba, da ginshiƙi...

Yadda akayiwa matar nan mai aman reza magani.

Amaryar nan da take aman reza da gashi da kuma aman jini,  yanzu Allah Ya bata lafiya. Ga masu sauraron gidan reriyo musamman a jihar Kano,  sun ji yadda wata Amarya ta kai kuka gidan rediyo akan yadda take fama da wani irin amai. Wato tana aman reza ne tare da jini,  kowace reza an karyata gida biyu,  ahaka take fadowa daga bakinta kuma tana jin rezar tana yanka mata makogwaro. Abin bai tsaya anan ba,  tana ganin an yanke mata gashin kanta, idan tay mai kuma sai aga gashin kan nata acikin aman. Haka dai Amaryar ta dinga fama da yawan tashin gobara kuma tana zabura ta fita aguje,  har sai an sa an kamota. Abin tausayin bai tsaya anan ba,  domin jini yana yin tsattuwa daga babban dan yatsanta da kuma le6enta bakinta na qasa. Baya ga mugayen mafarkai da take fama da su, duk da cewa ga ciki tana dauke da shi. Wannan dalili yasa wata baiwar Allah tay musu jagora zuwa gidan rediyon RAHMA RADIO da ke Jihar Kano,  su kuma suka turota cibiyar Tarbi...