YAƘIN UHUDU

Yaƙi na biyu da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya je da kansa

Daga Shafin Bashir Halilu.

      A cikin babban littafin tarihin nan mai suna 'Albidayah Wannihayah' wanda Shaihun Malami Ibnu Kasir ya wallafa, ya kawo cewa:

   Bayan an gama yaƙin Badar, wanda jama'ar musulmi su ka yi ƙoƙarin tare tawagar dukiyar Ƙuraishawan Makkah; dukiyar da aka tabbatar cewa dukiyar musulmai ce da su ka bari a Makkah Ƙuraishawa su ka deɓe musu, suke kasuwanci da ita. A ƙarshe ƙwace dukiyar bai samu ba domin Abu Suf'yan da ke jagorantar tawagar dukiyar ya gane ana bibiyarsa, don haka  ya canja hanya, ya gudu.

       Duk da ba a samu ƙwace dukiyar ba, Ƙuraishawa sun fito, inda aka haɗu a Badar aka gwabza yaƙi kuma Musulami su ka samu gagarumar nasara. Wannan ya sa Ƙuraishawa su ka sake shiri bayan shekara ɗaya da wannan yaƙi, su ka sake dawowa domin ɗaukar fansar abinda Musulmai su ka yi musu a yaƙin Badar. Daga cikinsu akwai Abū Sufyān, wanda ya rantse cewar ba zai zauna lafiya ba har sai ya rama abinda aka yi musu a Badar.

         A cikin watan Shawwāl na shekara ta 3 bayan hijira, Ƙurayshawa su ka kwaso mayaƙa kimanin mutum dubu uku (3,000) su ka nufo Madīna. 

        A cikin wannan runduna akwai shahararrun mayaƙa irin su Abū Sufyān, Khalid ibnul-Walīd da 'Amru ibnul-‘Āṣ.

     Ƙuraishawa sun nufo dutsen Ʋḥud, wani babban dutse ne da ke arewacin Madīna.

       Ko da aka samu labarin zuwansu, sai  Manzon Allah ﷺ ya shawarci sahabbansa cewa  "Shin mu zauna a cikin Madīna, mu jira su, ko kuwa mu fito mu fuskance su a fili?"

     Wasu daga cikin Sahabbai  sun ba da shawarar su zauna cikin birnin, su baiwa Madina kariya, amma matasa da jarumai, musamman waɗanda ba su halarci yaƙin Badar ba, su ka ce: “Ya Manzon Allah, mu fito mu fuskance su!”

      Manzon Allah ﷺ ya amince da shawarar matasa. Ya shirya rundunarsa, ya fitar da mutane kusan 1,000 aka fita domin tarar tawagar arna. Amma a tsakiyar hanya, ana cikin tafiya, sai wani babban munafuki, wanda  ba Musulmin gaske ba ne, mai suna ‘Abdullāhi ibn Ubayy bin Salul', ya janye mutane kimanin 300 daga rundunar, yana cewa ya fasa zuwa yaƙin, shi dama bai amince da tafiyar ba tun farko, don haka su ka koma gida.

    Sai ya rage saura mayaƙa ɗari bakwai (700) kacal, yayinda arna kuma sun kai mutum dubu uku (3000). 

    Duk da haka Manzon Allah ﷺ ya cigaba da tafiya, tare da tsara yadda rundunar za ta kasance a filin yaƙi. Ya keɓe mutum hamsin (50) daga cikin ƙwararru wajen iya harbi da kibiya, ya sa su a wani tudu da ake kira 'Jabalur Rumātu', ya ce da su "Kada ku sauko daga tudun nan, ko mun ci nasara ko an ci nasara a kanmu, ku tsaya a wurin!”

        Haka aka haɗu gaba da gaba da tawagar arnan Makkah, aka fara gwabza faɗa. Yaƙin ya fara da bayyanar ƙwazon musulmai, su ka karya gwiwar Ƙurayshawa, su ka fara kore su daga fagen fama. 

        Manyan jarumai kamar su ‘Alīyu ibn Abī Ɗalib, Abū Dujāna, da Hamza ibn ‘Abdul-Muɗɗalib su ka shiga filin fama da gagarumar jarumta.

    Hamza, wanda ake ce wa Zakin Allah, kuma yaya ne ga Mahaifin Manzon Allah (SAW), ya kashe maƙiya da dama. 
      Daga can saman dutse kuwa maharban musulmai ne ke ta ruwan kibiyoyi akan arna, ƙasa azaba sama azaba. Ana cikin haka ne, mayaƙan Ƙuraishawa su ka fara ja da baya, suna guduwa.

    Da masu harbin nan da ke kan dutse suka ga cewa Musulmai sun ci nasara, arna sun gudu, sai su ka dinga saukowa daga saman dutsen, suna tattara kayan da arna su ka zubar, suna tara ganima. Shugaban waɗannan maharba ‘Abdullāh ibn Jubayr, ya tunatar da su da umarnin Manzon Allah (SAW) cewa kada su sauka ko da sun ci nasara amma sai su ke ganin kamar ba matsala, su sauka, sai wasu ƴan ƙalilan kawai a saman dutsen.

  Wannan kuskuren da su ka yi ya ba Khalid ibnu -Walīd,  ɗaya daga cikin kaftin ɗin mayaƙan Ƙurayshawa da ke leƙen gefe damar juyowa ta baya da rundunarsa, su ka danno ta baya, babu mai hango su daga sama, su ka rutsa musulmai a bango. Fagen ya rikice, nan da nan yaƙi ya sauya salo, aka fara kashe mayaƙan Musulmai.

    Daga nan aka kashe Hamza, wanda wani bawa mai suna Wahshī, dan ƙasar Habasha, ya caka masa mashi, kamar yadda uwar ɗakinsa mai suna Hindu, matar Abū Sufyān, ta umarce cewa indai ya kashe Hamza to za ta ƴanta shi, don ramuwar gayya bisa mutuwar babanta a yaƙin Badar da aka yi shekarar da ta wuce.

    Yaƙi yai tsanani sosai, har wasu daga cikin arna su ka dinga ihu cewa Annabi Muhammad (SAW) ya rasu. A cikin ruɗani wasu daga cikin Musulmai su ka durƙusa, wasu su ka janye, wasu suka fāɗi bisa gwiwa. Musulmai sun ga damuwa sosai a wannan lokaci.

     Amma wasu jarumai kamar Ɗalḥatu bin ‘Ubaydillāh, Sa‘d ibn Abī Waƙƙāṣ, da Anas ibn Naḍr su ka tsaya tsayin daka suna kare Manzon Allah har su ka ji raunuka masu tsanani. An raunata bayin Allah masu daraja a wannan yaƙi kuma an zubar musu da jini.

    Bayan wannan fafatawa, duk da ruɗanin da musulmai su ka shiga na karyewar yaƙi, kafiran Makkah sun ƙi yarda su shiga cikin Madīna, domin suna jin tsoron ramuwar gayya. Su ka tsaya a waje, sannan suka fice suka koma gida. 

     Musulmai su ka tattara gawarwaki, su ka binne shahidan yaƙin, ciki har da Hamza, wan mahaifin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam.

    Manzon Allah ﷺ ya tsaya a bakin kabarin Hamza, yana kuka da zuciya cike da baƙin ciki, yana cewa "Ba wanda ya yi mini alheri fiye da Hamza.”

     Daga cikin abun mamaki da Allah Ya ƙaddara a wannan yaƙi shi ne, dukkan wani babban kafiri da aka ambata, wanda yay ɓarna ga musulmai a yaƙin nan na Uhudu ,to daga baya ya musulunta kuma ya zama sojan musulunci.

Misali, babban kwamandan yaƙin, Abu Suf'yan, ya Musulunta ranar Fat'hu Makkah.

    Babban sojan da ya rutsa musulamai yai musu ɓarna, Khalid Ibnu Walid, ya musulunta, har Annabi (SAW) yana yi masa kirari da 'Takobin Allah'.

  Wanda ya kashe Hamza, Wahshiy, ya musulunta, har ayar Alƙur'ani ce ta sauka a kansa, sannan Annabi (SAW)  ya aika a gaya masa cewa ya zo Allah Ya yafe masa.

   Wacce ta sa aka kashe Hamza, Hindu, matar Abi Suf'yan, ta musulunta.

     Ƙwararren mayaƙi da ya zo a cikin tawagar arna, Amru binil Asi, ya dawo har Madina da kansa, ya musulunta tare da abokansa guda biyu.
      Alhamdu lillahi.


Daga shafin Bashir Halilu

Comments

Popular Posts