Posts

Showing posts from April, 2018

DANNAU. DANNAU A LOKACIN BACCI. ALJANI MAI DANNE MUTUM LOKACIN DA YAKE BACCI.

Image
MENENE DANNAU? Dannau shi ne lokacinda mutum ya kwanta yana bacci,  sai ya ji kamar an zo an danne shi,  an shake masa hanci da baki,  ba ya iya motsi ko numfashi ko magana kuma yana ihu amma ba a ji. Mutum ya kan cika da tsoro da tunanin mutuwa lokacinda abun yake faruwa da shi. Kashi uku zuwa shida bisa dari (3-6%) na mutanen duniya suna fama da matsalar Dannau. Yayinda kashi talatin bisa dari (30%) na matasa kuma suna fama da wannan matsala,  aqalla kowanne acikinsu ya ta6a fuskantar matsalar Dannau ko da sau daya ne a rayuwarsa. Daga shafin Bashir Halilu Tarbiyyah Islamiyyah,  masu yin Ruqiyyah da harhada magunguan musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846. بسم الله الرحمن الرحيم وصلى الله على النبي الكريم. A gargajiyar Bahaushe,  Dannau wani Aljani ne da yake zuwa ya hau kan mutum lokacin da yake bacci,  ya shaqe shi,  ya hana shi sukuni. A binciken da Cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah ta gudanar,  ta gano wadansu abub...