YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN ALJANU
MAGUNGUNAN DA KE KONA ALJANI DA KASHE SHI.
Daga cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah masu yin Rukiyyah da harhada magungunan
Musulunci. Lambar waya +2348162600700, +2348134434846.
.
1- A samu Kaikayi-koma-kan-mashekiya, tazargade, jema, hiltit da nono. Sai a hada
su waje daya a dafa. Idan an dafa sai a raba biyu, rabi a dinga zubawa a nono ana
sha, rabin kuma a dinga yin wanka da shi. Yana maganin farfadiya da Jinnul katfa masu make mutane, da ciwon 6arin jiki wanda Aljanu su ka haifar.
.
2- Kwankawatsen mahauta, tsamiyar makiyaya, da bakin bunu. Sai a hada su waje
daya a dinga hayaki da shi a jiki kullum, don maganin bakaken Aljanu. Yana kuma hana Aljanu shiga gida da ra6ar wajen da aka turara saidai yana karya magunguna marasa karfi da suke kusa da shi.
.
3- Ma'ul wardi, ma'ul khal da kuma alkahauli, sai a hada su waje daya, a hada da ruwa kadan a dinga shafe jiki da shi. Yana toshe hanyoyin da Aljanu suke shiga jikin mutane yana kuma fitar da su cikin gaggawa.
.
4- Tsakin kuka, bintil sudan, sassaken dogon yaro da kuma furen tumfafiya. Sai a hada su waje daya a daka, a jika a cikin turaren, a dinga shafe jiki da shi. Sariqul jinni, rariyar hannu da namijin dare, duk wannan hadin yana maganinsu.
.
5- Ma'ul wardi, ma'ul khal, hiltit da zuma. A jada su waje daya, a dinga zubawa a ruwa, ana sha, kullum sau daya. Idan Aljanu suka rikewa mutum baki ya kasa magana bakin zai bude. Yana maganin ciwin ciki da kirji da mara, wadanda Aljanu suka haifar.
.
6- Jan kajiji, bakin kaji, habbatus saudaaa, habbatur rashad, farar wuta da kuma tafarnuwa. A hada su a daka. Sai a raba biyu, rabi a kwa6a da man kadanya a dinga shafe jiki da shi, rabin kuma a dinga yin hayaki da shi. Yana maganin ciwon daji da kansar mama da fatar da Aljanu suka 6ata. Yana hana Aljanu shiga jikin mutum yana kuma korarsu daga gida.
.
7- Nonon giwa, jan miski, kustul hidiy, farar wuta, man gelo, da ma'ul khal. A hada su waje daya, sai a dinga shaka, kullum sau uku. Yana fitar da Aljani daga jikin mutum nan take. Yana maganin ciwon kai da ciwon kirji wadanda Aljanu su ka haifar yana kuma saurin kona Aljani da kashe shi.
.
8- Turaren Ambar, turaren za'afaran, jan miski, bakin miski, da kuma man juda. A hada su waje daya, a dinga shafe jiki kullum idan za a kwanta barci da adaddare. Yana maganin namijin dare da mugwayen mafarkai da figita da rashin barci wanda Aljanu su ka haifar.
.
9- Man juda, habbatus saudaa, man zaitun, man gelo, zuma da man tafarnuwa, a hada su waje daya, a dinga shan cokali daya kullum. Yana saurin kashe Aljani har lahira, yana magani cututtuka da Aljanu su ka saka a jikin mutum.
.
10- Bakin hayaki, bakin bunu, da kuma baduhun shuri. A hada su waje daya, a dinga hayaki kullum sau biyu amma hayakin daki da gida ake turarawa. Yana korar Aljanu da suke zaune a gidan mutane ko wajen aiki sannan yana fitar da Aljani daga jikin mutum.
.
11- Turar ruwa, gashin jima, Fusuhul jinni, da hiltit. A hada su waje daya, a dinga hayaki kullum sau daya. Wannan hadin yana karya sihiri yana maganin yawan faduwar gaba da 6acin rai mara dalili da ciwon kan lokacin magriba da jin haushin mutane ba dalili.
.
12- Buruku, ganyen raidore, duman rafi da kaikayi-koma-kan-mashekiya. A tafasa a dinga sha da wanka. Maganin Kowace irin lalura ta Aljanu wacce ta shafi cikin jiki.
.
13- Sassaken gawo, kaikayi koma kan mashekiya, sassaken katsari. A dafa, sha da wanka. Yana magani sammu da maita da baki da kambun ido.
.
14- Ganyen sarkakiya, ganyen sidr da garin sabara. A dafa su tare, a dinga sha. Maganin kowace cuta ta jinnu wacce take cikin jiki.
.
15- Sabulun zaitun, sabulun habba, tafarnuwa, ganyen magarya da jan miski. A hada sabulan waje daya, sai a kir6a tafarnuwa a zuba ma ta ruwa a matse, a zuba acikin sabulun da turaren a dinga wanka da shi. Yana gyara fata wacce Aljanu su ka 6ata sannan yana toshe hanyoyin da Aljani ke bi domin shiga jikin mutum.
.
16- Bakin magani, sanamakiy, garin sabara, da kuma garin rawaya kadan. Sai a tafasa da lemon tsami ko tsamiya, idan ya huce a dinga sha. Maganin kowacce laurara wacce Aljani ya saka a cikin jiki.
.
17- Ganyen kaba da kuma jema. A jika su a sabuwar tukunyar kasa a dinga sha. Yana maganin fitsarin kwance na manya da yara, yana maganin maita da Aljanu mazauna cikin gida.
.
18- Shuhurul jinni, du'a'ul jannnah da muhriqul jinni. A daka muhriqul jinnin a jika shi acikin turarukan, a dinga shafe jiki da shi. Yana maganin Aljani mai taurin naci, yana hana shi shiga jikin mutum.
.
19- Azfarul jinni da shajaratu Maryam. A jika su tare a dinga sha. Magani ciwon ciki, matsalar nakuda, kwanciyar ciki da yawan 6ari. Tana bin Aljani duk inda ya shiga ajikin mutum ta fitar da shi cikin sauki da yaddar Allah.
.
20- Kanwa, gishiri da albasa. A hada su waje daya, a jika a cikin kwarya, a dinga sha. Yana magani cutar Aljani tare da karya sihiri cikin sauki.
.
21- Farin hayaki, tazargade, ganyen kaba, da habbatussauda. A hada a dinga hayaki da su. Maganin namijin dare, maita da sauran cututtukan Aljanu.
.
22- Ganyen na'ana'a, raihan, jema, zuma da kuma garin bakin bunu. A dinga dafawa ana yin shayi da su. Yana maganin rashin gane karatu, shirita da fitar da sihiri daga jikin mutum.
.
23- Kamfani, bintil sudan, jan miski, shuhurul jinni, ma'ul jinni. A hade su waje daya, a dinga shafe jiki da shi. Yana hana Aljani shiga shiga mutum yana kuma fitar da wanda yake ciki.
.
24- Kafoor mash'hoor, gadali, man kadanya a hada waje daya a dinga shafawa a hannu da kafafuwa. Yana toshe hanyoyin da Aljani yake bi domin shiga jikin mutum.
.
25- Ganyen aduwa, ganyen magarya, ganyen dinya da ganyen sarkakiya. A dinga dafawa, sha da wanka. Maganin kowace irin cutar Aljani ta cikin jiki.
.
26- Garin sanya, hannu, fasakwari, sassaken 6aure, bakin magani. A dafa a dinga sha amma sanyar kadan ake zuba ta. Maganin fitsarin kwance, firgita da mugwayen mafarkai.
.
27- `Ya`yan zurman, bakin algaru, jan algaru ganyen tumfafiya. A hada waje daya a dinga turarawa acikin gida da cikin dakuna. Yana korar Aljanu daga gida kuma yana hana Aljanu shiga gidan.
.
28- Jan miski. `ya`yan zurman, man juda, Kafoor mash'shoor. A hada su waje daya a dinga shafawa a ga6o6in jiki guda talatin. Yana toshewa Aljani hanyar shiga jikin dan'Adam.
.
Daga cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah, masu yin rukiyyah da harhada magungunan musulunci. Lambar waya +2348162600700, +2348134434846.
.
AMMA A KULA
Ya kamata duk wanda zai yi amfani da wadannan magunguna to ka tuntu6i masani akan fannin magani domin yay maka bayanin gwargwadon yadda za kay amfani da kowanne sannan a ware ma ka maganin da mace mai ciki ba ta sha da wanda ba a baiwa kananan yara da dai sauran dokoki da su ka danganci magani.
.
Ga wanda yake bukatar wadanda muke hadawa.
Muna sayarda dukkan magungunan da mu ka ambata, muna sayarda wadanda aka riga aka hada su, amfani kawai za kay da su. Kamar Magungunan sha, da na shafawa dana hayaki dana fesawa a cikin gida da dai sauransu. Za a iya tuntu6armu a lambobin waya +2348162600700 da kuma +2348134434846.
Muna yin rukiyyah tare da hada magungunan musulunci.
.
Daga shafin Bashir Halilu Tarbiyyah Islamiyya.
.
.
WhatsApp & call +2348162600700, +2348134434846.
Allah saka da alheri
ReplyDeleteAllahu yasaka da mafificin alkhairi
ReplyDeleteMuna godiya
ReplyDeleteAllah ubangiji ya saka maku da gidan Aljannah.
ReplyDeleteAllah yasaka Miku da alkairi
ReplyDeletehttps://mynovels.com.ng/gidan-uncle-episode-1-audio/
ReplyDeleteAslm, Allah yasakamaku da gidan Aljanna .
ReplyDeleteAllah ya biya ku
ReplyDeleteKhadiza..ahmad.
ReplyDelete07069272039
ReplyDeleteAllah .yasaka dalkaire
ReplyDeleteJazaka Allahu Khairan katheeran Malam Bashir.
ReplyDeleteNa ilmantu kwarai. Allah ya saka da alkhairi. A ina za'a sameka in ana bukatar ganinka? Na gode.
DeleteALLAH YASAKA DA ALHERI
ReplyDeleteMuna godiya dawanna hiddima
ReplyDeleteMasha'Allah Allah yasaka da alkhairi
ReplyDelete