HAƊUWAR SHAIƊAN DA ANNABI ISA (A.S.)
Daga Shafin Bashir Halilu. An karɓo daga Abu Bakar Muhammad ya ce: Al-Fablu bin Musa al-Baṣri ya ba mu labari, ya ce: Ibrāhīm bin Bashshār ya ce: Na ji Sufyān bn ‘Uyaynah yana cewa: "Annabi Isa ɗan Maryam (A.S) ya haɗu da Iblīs, sai Iblīs ya ce masa: — “Kai ne wanda saboda girman allantakarka ya kai ga cewa ka yi magana tun kana jariri a cikin zanin goyo, alhali babu wanda ya taɓa yin magana a cikin zanin goyo kafin kai." Sai Annabi Īsā (A.S) ya ce da shi “Ai matsayin Allantaka da girma na Allah ne, wanda Ya sa na iya magana. Shi ne kuma zai kashe ni, sannan Ya raya ni.” Sai Iblīs ya ce “To kai ne wanda girman allantakarka ya kai har kana ta da matattu” Sai Annabi Isā (A.S) ya ce: “Ai matsayin Alkantaka na Allah ne, wanda Zai kashe ni, kuma Ya kashe waɗanda na ta raya, sannan Ya raya ni.” Sai Iblīs ya ce: “Na rantse da Allah, kai Allah ne a sama, kuma Allah ne a ƙasa!” ...